Wane ne yake lura da shafin Facebook?

Facebook is ramping up its human staff in order to combat growing levels of inappropriate content

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Facebook na kara yawan ma'aikatansa domin yakar hauhawar sakonnin da ba su dace ba

Mark Zuckerberg ya gana da majalisar dokokin Turai a ranar Talata, inda ya sake bayar da amsoshi game da tambayoyi kan yadda kamfaninsa zai dakile wata badakala kan amfani da bayanan masu amfani da Facebook ta yadda bai dace ba.

Daya ne daga cikin rikice-rikicen da suka dabaibaiye kamfanin cikin watannin nan, daga farfagandar Rasha zuwa kalaman nuna kiyayya.

A wani yunkuri na kwantar da hankali game da fargabar da ake, zai sake mayar da hankali game da cewa Facebook na daukar ma'aikata da yawa.

Dubban sabbin ma'aikata aka dauka domin su kara sa ido game da yadda ake tantance sakonni wanda komfuta ba za ta iya yi ita kadai ba.

Kamfanin ya ce a yanzu yana da mutum 15,000 cikin wadanda suke kokarin kare masu amfani da kafar Facebook.

Kuma yawan mutanen da kamfanin ke bukata na kan hanyar zuwa 20,000. Wannan ya ninka adadin mutanen i war haka bara.

Wadannan su ne mutanen da aka bai wa alhakin zama masu kariya daga bata-garin masu amfani da Facebook, kuma wasu na ganin abu ne mai muhimmi cewa ya wakilci jama'ar da suka fi kasancewa cikin hatsari a intanet.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mark Zuckerberg ya shaida wa majalisar dokoki cewar zai kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa kan bambance-bambance da kuma hakkin dan adam

"Yana da matukar muhimmanci masu yin wannan aiki su fito daga wurare daban-daban da kuma sannin bambance-bambance tsakanin masu tace bayanan," in ji Brandie Nonnecke, darakta a sashen CITRUS da ke nazari kan amfani da fasaha domin amfanin jama'a a Jami'ar California.

"Yawan bambance-bambance da ake da su tsakanin masu tace bayananka shi zai sa su kasance masu ilimi game da abubuwan da za su kasance kalaman kiyayya ko kuma akasin haka tsakanin wadanda ke amfani da shafin Facebook."

Babu bayanai kan bambance-bambance

Da wa da wa ne mutanen?

Abu ne mai wuyar ganowa, saboda sarkakiyar da ke tattare da yadda Facebook ya dauki dubban mutane cikin gaggawa.

Mutum 15,000 da kamfanin ya dauka kawo yanzu ba wadanda suke cire sakonnin ba ne kawai - da aka sani da sunan masu bibiyar sakonni - amma har da injiniyoyi, masu nazari kan bayanai, da kuma wasu ayyukan da suka jibinci wannan.

Masu tantance sakonni kawo yanzu dai sun kai 7,500 - ma'aikata da ke kan gaba wajen yanke hukunci kan sakon da za a bari da kuma wadanda za a cire daga Facebook, idan komfuta ba ta kama shi ba da farko.