Babu wanda ya isa ya ga baya na – R Kelly

R Kelly
Bayanan hoto,

Ana zargin mawakin da cin zarafin wasu mata sai dai ya musanta zargin

An dauki hoton bidiyon shahararen mawakin R&B din nan R Kelly a cikin wani daki mai cike da mutane yana fada musu cewa "an makara" a kokarin da ake yi wajan ganin an dakile tasirin wakokinsa.

A ranar 17 ga watan Mayu ne aka wallafa bidiyon a shafin Facebook yayin da mawakin ke fuskantar sabuwar tuhuma kan cin zarafin mata ta hanyar lalata.

"Babu wanda ya isa ya ga bayana," in ji shi, ya na rike da tabar sigari. "A cikin shekara 30 da ta gabata ne ya kamata su yi haka.

"Sun makara. Wakokina sun riga sun samu karbuwa a duniya."

An shafe shekaru ana tuhumar R Kelly da cin zarafi ta hanyar lalata ciki har da yin lalata da 'yan mata da shekarunsu ba su kai 18 ba da kuma zargin da a ke yi masa kan cewa ya "kafa wani gungu na masu yi wa mata fyade" sai dai ya musanta zargin .

Shahararen mawakin wanda bakandamiyarsa ta hada da I Believe I Can Fly da The World's Greatest, ya musanta zargin da ake yi masa na aikata ba dai dai ba; sai dai martabarsa da kuma harkokin kasuwancinsa sun fuskanci koma baya a makonnin baya-bayan nan sakamakon wani gangamin adawa da aka bullo da shi mai taken #MuteRKelly.

Gangamin na kokarin hana mutane sauraron wakokin R Kelly sakamakon zargin da ake yi masa ne kuma sun nemi kamfanonin da ke tallata wakokinsa da kuma masu sayar da tikiti akan su janye goyon bayan da suke nuna masa.

Sabuwar tuhumar da ake yi wa R Kelly

Kamfanin tallata wakoki a shafin intanet Spotify ya cire wakokinsa daga kundisa tun daga ranar 10 ga watan Mayu (kodayake har yanzu ana samun wakokin a shafin).

Shi ma kamfanin tallata wakoki na Apple ya yi shelar daukar mataki irin wannan.

Bayanan hoto,

Faith Rodgers na zargin mawakin da cin zarafinta ta hanyar lalata da zagi

A bidiyon da aka wallafa a shafin Facebook wanda kamfanin watsa labarai na The Grio ya rawaito, an nuna lokacin da Mr Kelly ke yi wa wasu mutane jawabi inda ya ke cewa "Akwai mutane miliyan daya da ba sa kaunata kuma ina da mutane biliyan 40 masu so na."

Ya jinjina wa maza da suka nuna "karfin hali "da ke cikin dakin .

"Saboda mutane irinku ne na ci gaba da abin da na ke yi saboda tunani na irin na masu wasan kwallon kwando ne," in ji shi, muddin ina rike da kwallo a hannu na, toh duniya za ta ja baya".

Bayan da aka fitar da bidiyon a ranar Litinin wata mata daga Texas ta shigar da kara a gaban kotu inda take zargin R Kelly da cin zarafinta ta hanyar lalata da ita tare da kuma saka mata ciwon sanyi.

Faith Rodgers ta ce shahararren mawakin ya ci zarafinta ta hanyar dukanta da zagi a shekara fiye da guda da suka yi suna soyayya.