An yi fim game da kalaman Buhari kan matasa

Fim din cima-zaune

An shirya sabon fim game da kalaman Shugaba Muhammadu Buhari da suka ja hankalin matasa a Najeriya.

Fim din mai taken "cima-zaune" yana bayani ne game da kalaman da shugaban ya yi cewa da dama daga cikin matasan kasar 'yan-tamore ne kawai, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

A kalaman na watan Afrilu, shugaban ya bayyana cewa mafi yawan matasan Najeriya ba su yi karatu ba, kuma ba su da aikin yi, sannan suna jira gwamnati ta samar mu su abubuwan more rayuwa kyautai.

Wadanda suka shirya fim din sun ce sun yi hakan ne saboda yadda kalaman suka ja hankali a ciki da wajen kasar, sannan suka haifar da ce-ce-ku-cen siyasa.

Furodusan fim din Hamza Lawal Abubakar da aka fi sani da Dogo Dandago, ya shaida wa BBC cewa an shirya fim din ne da nufin fadakar da jama'a game da muhimmacin kamalan shugaban.

Abba Al-Mustapha wanda ya fito a matsayin babban tauraron fim din, ya shaida wa wakilin BBC Pidgin Mansur Abubakar cewa sun lura ne da matsalar cima-zaune a tsakanin matasa a zamanin yau.

Ya kara da cewa sakon Fim din ya bada labarin wani matashi da ya shafe shekaru biyar yana neman aiki da kwalin digirinsa a fannin injiniyarin, amma da aikin ya gagara sai ya zo ya hadu da wasu abokanai da ba a abin da suka sani sai cima-zaune.

Image caption Cikin wadana suka fito a fim din har da Sulaiman Bosho

"Yawanci za ka ga cewar matasa sun hakura da karatu da duk wasu abubuwa na neman kudi, sun koma suna dogaro da gwamnati da manyan 'yan siyasa," a cewar Al-Mustapha, wanda ya fito a matsayin Rayyan a sabon fim din.

Ya kara da cewa fim din ya kalubalanci irin zaman rayuwar matasa a yanzu tare da fadakar da su kan yadda za su tashi su nemi na kansu ko da kuwa karamar sana'a ce ba lalle sai mutum ya samu aiki ba.

Kawo yanzu ba a bayyana ranar da fim, wanda ake ci gaba da nada zai fito ba.

Ba ya ga Abba Al-Mustapha, akwai karin wasu taurarin na Kannywood da suka fito a fim din ciki har da Sulaiman Bosho.

Image caption Jaruman fim din cima-zaune a lokacin da ake nadar wani bangare nasa