Hotunan yadda wani jirgi ya fado ya rabe biyu

Dukkan fasinjojin cikin jirgin sun rayu, bayan da jirgin da ya dauko su daga birnin Texas na Amurka zuwa Honduras ya fadi ya kuma rabe biyu.

Bayanan hoto,

A kalla Amurkawa shida ne suka ji rauni yayin da jirgin ya fadi a Tegucigalpa babban birnin kasar Honduras a ranar Laraba da safe.

Bayanan hoto,

Jirgin mai suna Gulfstream G200 ya taso ne daga garin Austin na Texas, yayin da ya zarce daga titin saukar jirgi na Toncontin.

Bayanan hoto,

Har yanzu hukumomi ba su fadi adadin mutanen da ke cikin jirgin, wadansu sun ce shida ko tara.

Bayanan hoto,

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya taimaki maza biyar da wata mata fita daga jirgin, amma babu wanda ya ji rauni a cikinsu.

Bayanan hoto,

Wani jami'in gwamnati ya shaida wa kafofin watsa labarai na Honduras cewa babban jirgin na musamman, wanda ya rabe biyu, ya shiga cikin rami.

Bayanan hoto,

Filin jirgin saman Toncontin na kewaye da manyan duwatsu da titin saukar jirgi mara tsayi sosai.

Bayanan hoto,

A shekarar 2008, wani jirgin saman TACA ya fadi a kusa da inda wannan jirgin ya fadi. Amma mutane biyar sun rasu a wancan hadarin.

Bayanan hoto,

Gwamnatin kasar na gina wani sabon filin jirgin saman mai nisan kilomita 50 daga babban birnin.