Iyaye sun kai dansu kotu saboda ya ki bar musu gida

Michael Rotondo ya je Kotu a ranar 22 ga watan Mayu
Bayanan hoto,

Michael Rotondo, mai shekara 30, ya je kotu ranar Laraba

Iyayen wani matashi dan shekara 30 sun kai shi kara kotu saboda ya ki bar musu gida, bayan da ya kai munzalin yin hakan a ganin su.

Takardun kotu sun nuna cewa matashin mai suna Micheal Rotondo, ba ya biyan kudin haya, kuma ba ya taya iyayensa da ayyukan gida, sannan ya ki karbar kudin da iyayensa suka ba shi don ya je ya fara tasa rayuwar.

Bayan wasiku biyar da aka ba shi na kora, Christina da Mark Rotondo sun ce har yanzu dan nasu ya ki barin gida.

Michael yana musun cewa a bisa doka, ba a ba shi cikakken wa'adin barin gidan ba.

Mista da Misis Rotondo sun kai kara a ne kotun kolin yankin Onondaga, kusa da Syracuse, a New York, a ranar 7 ga watan Mayu, bayan sun shafe watanni suna kokarin ganin dan nasu ya bar gidan.

Lauyan Micheal, Anthony Adorante, ya shaida wa kafar watsa labarai ta Syracuse.com, cewa ma'auratan ba su san wata hanyar da za su bi don sallamar dan nasu daga gidan ba.

Wasikar ta farko da aka karanta ranar 2 ga watan Fabrairu a kotun ta bayyana cewa: "Mun yanke shawara cewa sai ka bar gidan nan ba tare da bata lokaci ba."

Bayanan hoto,

Gidan iyayen dai na wani anki ne a birnin New York

Yayin da Micheal ya yi watsi da wasikar, sai iyayensa suka sake rubuta wasikar kora ta musamman tare da agajin lauyansu.

A wasika ta biyun da aka rubuta ranar 13 ga watan Fabrairu ta ce: "Don haka muka yanke shawarar korarka daga gidan nan."

"Za mu dauki matakin shari'a idan ba ka bar gidan nan ba zuwa ranar 15 ga watan Maris din 2018," a cewar wasikar.

Daga baya iyayen nasa sun ce za su ba shi dala 1,100 (kusan naira 400,000) ya bar gidan - tare da yayyaba masa bakar magana.

"Akwai ayyuka da irin ku da ba su taba sanin yadda ake aiki ba ma za su iya samu. Ka je ka nema - dole ka nemi na kanka!," in ji iyayen.

Amma a ranar 30 ga watan Maris, sai ta bayyana karara yaron ba shi da niyyar barin gidan.

A watan Afrilu ne Mista da Misis Rotondo suka je kotun kauyensu don ganin kotu ta kore shi daga gidan.

Sai aka gaya musu cewa sai sun samu izini daga Kotun Koli, ita za ta sa shi dole ya bar gidan tun da Micheal dansu ne.

Kamar yadda kafar watsa labaran WABC ta shaida, Micheal ya bayyana karar da iyayensa suka kai a matsayin ramuwar gayya kuma ya bukaci kotun ta yi watsi da ita.

Zuwa karshen watan nan, kotun kolin za ta yanke hukunci kan karar - makonni kadan kafin Micheal ya cika shekara 31.