Sojojin Najeriya na yi wa 'yan gudun hijira fyade - Amnesty

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Najeriya sun shafe shekaru 10 suna yaki da Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yi wa mata da kananan yara fyade wadanda suka tsere wa rikicin Boko Haram.

Kungiyar ta ce sojin na Najeriya na raba mata da mazajensu kuma suka yi musu fyade, wani lokaci suna ma su tayin abinci a sansanonin 'yan gudun hijira.

Dubban mutane ne suka mutu sakamakon yunwa a sansanonin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya tun 2015, in ji Amnesty.

Rundunar sojin Najeriya a cikin wata sanarwa ta yi watsi da rahoton na Amnesty.

"Dole ne a dakatar da irin wadannan rahotanni da ke rusa kyawawan ayyukan sojojinmu na kishin kasa," a cewar sanarwar rundunar sojin.

Dakarun Najeriya sun dade suna yakar 'yan Boko Haram tun 2009.

An kashe mutum fiye da 30,000 a rikicin, kuma kimanin mutane miliyan 1.8 rikicin ya raba da gidajensu.

Amnesty ta ce yanayin da ban tsoro inda mutanen da suka sha wahala a karkashin Boko Haram, sun kuma dawo suna ci gaba da shan wahala a hannun sojojin Najeriya.

"Maimakon samun kariya daga hukumomi, ana tilasta wa mata da 'yan mata fadawa tarkon fyade domin samun abincin da za su ci."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda sojoji suka ci zarafin mutanen Borno

Amnesty ta ce ta tattara shedar cin zarafi ne ta hanyar tarin bayanai da ta samu da hirarraki da wadanda aka muzgunawa a sansanonin 'yan gudun hijira tun daga shekarar 2015.

Kungiyar ta ce wasu mata biyar sun shaida ma ta cewa, an yi musu fyade a 2015 da kuma farkon 2016 a sansanin 'yan gudun hijira a Bama, a yayin da suka shiga wani yanayi na matsanancin yunwa.

Amma a sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta ce rahaton mataki ne da zai karya wa jami'an tsaro guiwa a yakin da suke yi da Boko Haram.

Labarai masu alaka