An bayar da belin Malam Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau da Mansur Ahmed
Bayanan hoto,

Ibrahim Shekarau (daga dama) ya mulki Kano daga shekarar 2003 zuwa 2011

Wata babbar kotu a Kano ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar bayan da aka gurfanar da shi tare da wasu mutum biyu bisa zargin halatta kudin haram.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau ne tare da Tsohon Ministan harkokin waje Aminu Wali da kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed.

Duka mutanen uku sun musanta tuhumce-tuhumce shida da aka yi musu da suka hada da karbar kudi daga jam'iyyar PDP a lokacin zaben 2015 duk da cewa sun san kudin ba ta halattacciyar hanya suka fito ba.

Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Mai shari'a Zainab Abubakar Bagi ta babbar kotu da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kano, ta bayar da belinsu a kan naira miliyan 100.

Wannan tuhuma na zuwa ne kwanaki kadan bayan hirar da Malam Shekarau, wanda dan takarar shugaban kasa ne a PDP ya yi da BBC, inda ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Magoya bayansa sun ce siyasa ce ta sa aka kama shi, amma gwamnatin ta sha musanta zargin hakon 'yan adawa a shirinta na yaki da cin hanci da rashawa.

Me ake tuhumarsu a kai?

Bayanan hoto,

Mutanen da ake zargi sun gurfana a kotun cikin kamala kamar yadda aka saba ganinsu

Hukumar EFCC ta tuhumi jiga-jigan na jam'iyyar adawa da aikata laifuka shida da suka shafi halatta kudin haram da hada baki, lamarin da dukkansu suka musanta.

  • Karbar kudi naira miliyan 950 daga uwar jam'iyyar PDP ta kasa
  • Sun san cewa kudin bai fito ta halattacciyar hanya ba - halatta kudin haram
  • Sun karbi kudin duk da suna da masaniya sun fito ne daga Tsohowar Ministar Mai Diezani Alison-Madueke
  • Ana tuhumar Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da ajiye kudin a wurinsu
  • Sannan suka raba kudin

Bayanan da mutanen suka yi shi ne cewa an raba kudin ne domin gudanar da ayyukan zabe na jam'iyyar PDP mai mulki a wancan lokaci kamar yadda uwar jam'iyyar ta nemi a yi.

Sun ce an raba kudin ne ga shugabannin jam'iyya a dukkan matakan jihar kamar yadda kowacce jam'iyya ta ke yi.

Wannan ya sa wasu ke tambayar cewa ko EFCC za ta bi dukkan shugabannin PDP a kananan hukumomin Kano 44 da suka karbi kudin domin kamo su.

Wakilin BBC a Kano, Ibrahim Isa, ya ce kotun ta cika makil da magoya baya 'yan siyasar, kuma sai da jami'an tsaro suka yi harbi sama da harba hayaki mai sa hawaye sannan aka tarwatsa jama'ar da suka taru a wajen kotun lokacin da za a fita su.

Ya kara da cewa mutanen uku sun isa kotun cikin shigar kamala kamar yadda suka saba yi, kuma babu wata alamar damuwa a tare da su.

Bayanan hoto,

Yadda 'yan sanda suka tarwatsa magoya bayan Shekarau a wajen kotu

Lauyoyin da ke kare bangarorin biyu sun kai ruwa-rana kafin daga bisani lauyan wadanda ake kara ya nemi belinsu.

Kuma ba tare da wata jayayya ba lauyan EFCC ya amince amma ya nemi a sauya sharudda masu karfi.

Bayan hutun dan lokaci, Mai Shari'a Zainab ta dawo inda ta bayar da belinsu kan kudi naira miliyan 100 da kuma samar da mutum uku da za su tsaya musu.

Daya daga cikin mutanen wajibi ne ya kasance ma'aikaci da ya kai mukamin darakta da kuma wanda ya mallaki babbar kadara a yankin da ke karkashin ikon kotun.

Sai a ranar 26 ga watan Yuni za a ci gaba da shari'ar.