Ba talakawa ba ne a zuciyar el-Rufa'i – Shehu Sani

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Martanin Sanata Shehu Sani kan kalaman Gwamnan Kaduna Nasir el-Rufa'i

Sanata Shehu Sani ya yi wa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa'i raddi kan kalamansa game da matsalar tsaro a Najeriya.

A cikin makon nan ne Gwamna el-Rufa'i ya shaida wa BBC cewa 'yan jarida ne ke zuzuta kashe-kashen da ake yi a kasar, tare da cewa kashe-kashen ba su taka kara sun karya ba.

El-Rufa'i ya ce "babu yadda za a yi a ce rashin tsaro a wani kauye ko wani gefe na kasa ya sa a ce duk kasar babu tsaro."

Amma a martaninsa, Sanata Shehu Sani ya ce babu yadda za a yi ace gwamna da ke da hankali da iyali da kuma kiran kansa yana da addini kuma yake cikin jam'iyyar da ta ke son ta kawo canji, ya ce "wai kisan gillan da ake yi wai bai kai ya kawo ba."

"Wannan abin takaici ne abin Allah wadarai ne, a ce wai gwamna guda, ya fito ya ce wai kisan gillan da ake yi ba wani abu ba ne a Najeriya," in ji Sanata Shehu Sani wanda suka jima suna takun-saka da gwamnan.

Ya kuma ce "hakan ya nuna gwamnan ba talakawa ba ne a zuciyarsa saboda yana ganin ba masu mulki ko masu hannu da shuni ba ne matalar ta shafa."

Sanatan ya ce magana ta farko da tsarin mulkin Najeriya ya fara da ita, shi ne hakkin gwamnati ne ta kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu, ba a fara da maganar wuta ko ruwa ko hanya ba ko kuma asibiti ba.

"Babu amfanin wadanda suke kan mulki idan ba za su iya kare 'yan Najeriya ba."

Ya kara da cewa "don suna tare da shugaban kasa suna inuwarsa, saboda haka duk abin da za su fadi ba su damu ba, za su iya taka kowa. Za su iya cin mutuncin kowa saboda sun tabbatar cewa za a sake zabensu."

An dade ana rikicin siyasa tsakanin bangaren gwamna el-Rufa'i da Sanata Shehu Sani, dukkaninsu 'yan jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya.

Rikicin bangarorin biyu har ya kai suna zagi da tofin Allah-tsine.

Kalaman el-Rufa'i sun janyo ce-ce-ku-ce

'Yan Najeriya sun ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman gwamnan na Kaduna Malam Nasir el-Rufa'i inda ya shaida wa BBC cewa 'yan jarida ne ke ruruta kashe-kashen da ake a Najeriya.

Mutane da dama ne suka bayyana ra'ayoyinsu tare da tafka muhawara a shafin Facebook na BBC bayan wallafa kalaman na gwamnan ranar Laraba.

Wadansu daga cikinsu sun goyi bayan kalaman gwamnan yayin da wasu kuma suka caccake shi tare da cewa ya cika banbarma.

Jihar Kaduna na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan fashi da yawaitar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.

A cikin mako guda an kashe mutane fiye da 50 a Kaduna tare da sace mutum da sama 130 a jihar.

Amma a cikin kalamansa, gwamnan wanda ke magana a wurin wani taron zuba jari a Abuja, ya ce bai kamata a ce duk Najeriya babu tsaro ba saboda ana fama da matsalar tsaro a wata jiha.

A nasa bangaren kuma, Sanata Shehu Sani ya ce "Idan wata kasa ce, gwamnan ba zai sake jin kamshin mulki ba a rayuwarsa ba, (bayan furta wadannan kalaman)."

Labarai masu alaka