An zabi Malala sakatariyar jin dadin dalibai a jami'ar Oxford

Malala Yousafzai ta tsaya lokacinda da aka bayana ta wakiliyar zaman lafiya ta MDD a ranar 10 ga watan Afrilu 2017
Bayanan hoto,

Matashiyar wadda ta karbi lambar yabo ta Peace Prize za ta yi aiki tare da wani a shekarar karatu mai zuwa

Matashiyar nan 'yar Pakistan wadda ta taba karbar lambar yabo ta zaman lafiya wato Nobel Peace Prize, Malala Yousafzai za ta taimaka wajen tsara yadda za a rika gudunar da shagulgula a Jami'ar Oxford, bayan da aka zabe ta sakatariyar jin dadin dalibai.

Matashiyar mai shekara 20 ta kammala shekara ta farko na karatun digrin da ta ke yi ne a jami'ar.

An zabe ta a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na jami'ar a zaben da aka yi a makon da ya gabata.

Malala wadda take karatun kimiyyar siyasa da falfasa da kuma tattalin arziki za ta rike mukamin ne tare da Tiger Akawin a shekarar karatu da ke tafe.

Shugabar kwamitin Lana Purcell, ta ce ayyukan da za su yi sun hada da Talata da kuma tsara yadda za a gudanar shagulgula a cikin jami'ar.

A shekarar 2012 ne, wani dan Taliban ya harbi Malala a ka da wuya da kuma kafada yayin da take dawo daga makaranta bayan ta rubuta wata kasida kan yadda rayuwa take karkashin mulkin masu tsatstsauran ra'ayin addini.

Bayan ta murmure daga munanan raunuka da ta ji ne, ita da iyalinta suka koma birnin Birmingham da ke kasar Birtaniya.

A watan Augusta na shekarar 2017 ne ta amince ta fara karatu a Jami'ar Oxford.

Ta kasance cikin tarurukan da aka yi a jami'ar.

Daya daga cikin tarurukan da kwamitin ya shirya a bana sun hada da kalon fim a sinima da sauraron kade-kaden Jazz da kuma wata liyafar da aka yi a cikin lambu.

"Ina fatan aiki tare da sabbin jami'an da aka zaba a shekarar karatu da ke tafe ," in ji Madam Purcell.