Yadda 'yan sanda suka tarwatsa magoya bayan Shekarau

'Yan sanda sun yi harbi sama domin tarwatsa magoya bayan tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano.

Bayanan hoto,

An baza 'yan sanda a gaban kotun da aka gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun yi harbi a sama da harba hayaki mai sa hawaye lokacin da aka fito da Shekarau bayan gama zaman kotun

Bayanan hoto,

Wakilin BBC yana cikin wadanda suka sha hayaki mai sa hawaye

Bayanan hoto,

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin hatta kudin haram

Bayanan hoto,

Duka mutanen uku sun musanta zargin da ake musu, kuma a yanzu an bayar da belinsu