'Na rinka shan kwaya 57 a kullum domin ta sani maye'

Zanen yatsu da kuma kwayoyin da ke sa maye

A watan Disamba na shekarar 2017 ne aka yanke wa wata 'yar Birtaniya Laura Plummer, hukuncin daurin shekara uku a gidan yari bayan da aka sameta da laifin shigar da kwayar Tramadol 300 cikin Masar.

Sai dai yayin da hukuncin ya bai wa mutane da dama mamaki a Birtaniya, amma shari'ar ta fito fili ta bayyana yadda girman matsalar take da yadda take shafar miliyoyin Misirawa.

Abdul Hameed mai shekara 24 ya tuna da lokacin da ya fahimci cewa yana shan kwaya fiye da kima.

"A lokacin shekarata 15 kuma muna buga game na PlayStation, sai wani ya zage ni, sai na dauki sanda na kwala masa a ka. Na rika ihu ina zagin kowa. Sai da na fasa tagogi."

Shekarar Abdul Hameed 13 lokacin da ya fara ta'ammuli da kwayar Tramadol a karon farko.

Kamar sauran matasa da ke kasar, ya fara ne da shan kashi daya bisa hudu na kwayar mai karfin miligram 100 domin ta sa shi maye.

Asalin hoton, Ahmed Maher

Bayanan hoto,

Abdul Hameed mai shekara 24 ya rika ta'ammali da kwayar Tramadol tun yana da shekara 13

"Na rika jin kamar ni jarumi ne," in ji shi. "Zan iya yin duk wani abin da nake so."

Sai dai a lokacin da ya fusata a wasan game din da suka yi, ya riga ya fara shan kwayoyi 57 na Tramadol da kuma wasu da ke sa maye.

'Gaskiya komin dacinta'

A cewar hukumar ya ki da masu ta'ammuli da miyagun kwayoyi da kuma samar musu da magani ta kasar, mutum miliyan 30 ne suke shan kwayoyin da ke sa maye kuma sun fi shan kwayar Tramadol.

Kwayar ta fara bayyanna ne a Masar cikin shekara 20 da suka gabata. Ta fi hodar ibilis arha kuma cikin sauki ake samunta a kemis, ta haka ta samu karbuwa cikin sauri daga wurin masu ta'ammuli da kwayoyi kuma ta bazu cikin al'umma, inda ake shanta domin rage zafin ciwo da kuma matsalolin rayuwa na yau da kullum.

Tramadol ta yi kamari sosai a Masar, kuma cibiyar kula da da masu ta'ammuli da kwaya da masu wannan matsala suke kira domin a kai musu dauki ta ce, tana samun kiran mutum 500 a ko wacce rana daga wadanda suke son su daina shan kwayar.

Asibitin kula da masu tabin hankali na gwamnati da ke Alkahira ya shaidawa BBC cewa, fiye da rabi na marasa lafiyar da take kula da su shekarunsu ya kai 21 zuwa 30.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

An yanke wa Laura Plummer yar Birtaniya hukuncin daurin shekara 3 a gidan kaso bayan ta shigo da Tramdol 300 ta haramtaciyyar hanya a Masar

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A cewar wata kididiga ta gwamnati kashi 70 cikin 100 na masu shan kwayar Tramadol maza ne, sai dai kuma ana samun karuwa a yawan mata masu ta'amali da kwayar.

Ahlam mai shekara 28, mahaifiya ce kuma ta fara shan kwayar Tramadol ne domin rage mata saurin gajiya da ayyukan gida da kuma kula da yara.

Ita ma ta fara ne da shan kashi daya bisa hudu na kwayar mai karfin miligram 100 kuma daga bisani ta koma ta shan kwaya hudu a ko wacce rana, amma yanzu ta ce kwayar ta daina tasiri a jikinta ko da ta kara yawan kwayoyin da take sha.

Ta ce: "Mijina ya bani kudi na sayi kaza, sai na fada masa cewa na saya amma yara ne suka cinye. Amma kuma ba haka ba ne, karya na yi masa. Na yi amfani da kudin ne domin na sayi Tramadol, su kuwa yara na dafa musu taliya. Wannan ita ce gaskiya."

Ahlam ta sayar da wasu kayan gidanta domin ta rika sayan kwayoyin da ke sa maye, kuma akwai lokacin da ta nemi wani makwabcinta a kan ya tara da ita, wanda shi ma yana ta'ammali da kwayoyi domin ya ba ta Tramadol amma ya ki.

Asalin hoton, Ahmed Maher

Bayanan hoto,

Sai an ba da takardar likita ake sayarda kwayar Tramadol a Masar

Kwaya ce da ake samu cikin sauki

Daya daga cikin dalilan da suka sa kwayar ta ke da kwarjini a Masar shi ne ana samunta cikin sauki.

Bisa ka'ida ana sayar da kwayar ne ga wanda ya zo da takardar asibiti, kuma masu kemis za su fuskanci hukuncin daurin shekara 25 a gidan kaso ida aka same su da lafin sayar da kwayar ba tare da takardar asibiti ba.

Sai dai masu ta'ammali da kwayoyin da ke sa maye sun ce ba a aiki da dokokin.

Dr Yasin Rajal, darakta ne a hukumar da ke sa ido kan ma su sayar da magani a kemis, kuma ya shaidawa BBC cewa ma'iakatar lafiya ta san hadarin da ke tattare da kwayar, kuma ta na kokarin ganin cewa ta dakile ayyukan masu sayar da ita ta bayan fage.

"Ma'aikatar lafiya na sa ido kan ma su kemis kuma tana aiki ne tare da ma'aikatar cikin gida wajen kai ziyara da kuma binciken ba zata."

'Kasuwar bayan fage'

Sai dai idan hukumomi sun hana masu kemis sayar da magani ba tare da takardar asibiti ba, masu ta'ammali da kwayar sun gano wata hanya ta samun kwayar.

Suna tuntubar likitoci inda suke korafin ciwon baya ko zafin wani rauni da suka ji yayin wasan motsa jiki, domin samun takardar asibiti da za su gabatar wa masu kemis daban-daban.

Asalin hoton, Ahmed Maher

Bayanan hoto,

A cikin mutane uku a Masar , daya daga ciki na ta'amali da kwayoyin da ke sa maye

Ana kuma samun kwayar a kasuwanin bayan fage.

Abdul Hameed ya kai wakilin BBC wata kasuwar bayan fage da ke Giza wanda shi ne gari mafi girma na uku a Masar, inda masu ta'amali da kwayoyin da ke sa maye suke zuwa zuwa su sayi kwayoyi.

Masu sayar da kwayoyin na yi wa mutane ihu a kan su tsaya a kan layi , an ajiye kwayar Tramadol ta hannun dama yayin da kwayar hodar ibilis da ganye wiwi na ta hagu.

Bude wani sabon babi

Abdul Hameed na fatan fara sabuwar rayuwa bayan da ya bar shan kwayoyin da ke sa maye.

A yanzu watansa ukuda barin shan kwayoyin da ke sa maye.

Yana samun kulawa a wani asibiti mai zaman kansa.

"Suna ba mu magunguna daban-daban wadanda a hankali suke aiki," in ji shi.

"Muna halatar taron bita kuma muna wasannin motsa jiki, kuma muna tattauna matsalolinmu. Ji nake kamar na koma sabon jariri."