An gano naira biliyan 10 a gidan tsohon shugaban kasa

Jamian 'yan sanda sun kwace kwalaye a wani gida da ke Kuala Lumpur, a Malaysia, a ranar 18 ga watan Mayu 2018.
Bayanan hoto,

'Yan sanda sun kwace kayan alfarma ciki har da jakunkuna da kayan kawa a samamen da suka kai a makon da ya gabata

Yan sanda a Malaysia sun gano tsabar kudi fiye da dala miliyan 28 (naira biliyan 10) da aka zuba a cikin jakunkuna a samamen da suka kai wa wasu gidaje da ake zargin suna da alaka da hambararren shugaban kasa Najib Razak.

Samamen na da alaka da binciken da ake yi a asusun samar da ababen more rayuwa watau 1MDB, inda a nan ne ake zargin cewa an sace kudin.

Ana tuhumar Mr Najib da yin sama da fadi da dala miliyan 700, sai dai a baya hukumomin kasar sun wanke daga aikata ba daidai ba.

Jam'iyarsa ta siyasa ta ce kudin da jami'an 'yan sanda suka gano, an ajiyesu ne domin yakin neman zabe.

Jam'iyyar United Malays National Organisation (Umno) ta ce a ciki akwai gudummuwar da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka bayar da kuma kudin da suka rage bayan da Mr Najib ya sha kayen da ya bada mamaki a hannun tsohon abokinsa Mahathir Mohammad a zaben shugaban kasa da aka yi a watan da muke ciki.

Sai dai a sanarwar da jam'iyyar Unmo ta fitar ta ce an soma shirye-shiryen mika kudin ga sabbin shugabannin jam'iyyar lokacin da da aka kwace kudin.

Ta ce jam'iyyar za ta sa a dawo mata da kudin domin ta yi amfani da su wajan sake farfoda da kanta bayan shan kaye da ta yi.

Bayanan hoto,

Yan sanda sun ce sun gano takardun kudi daban-daban har guda 26

Sabon bincike da aka yi a kan asusun 1MDB ya faru ne bayan da aka zabi Mahathir Mohammed.

Mr Najib ya amsa tambayoyi sau biyu a watan da muke ciki a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar.

Shugaban sashin binciken miyagun laifuka na hukumar Amar Singh, ya fadawa 'yan jarida cewa an gano kudin ne cikin jakunkuna 35 yayin da wasu 37 na dauke da agogo da kuma kayan kawa na mata.

Ya ce za a tantance darajar kayan nan bada jima wa ba.

A makon daya gabata ne lauyan Mr Najib ya ce mutumin da yake kare wa bai ji dadin "samamen" da aka kai masa ba.

"