Trump ya fasa ganawa da Kim Jong-un

Trump da Kim Jong-un

Shugaban Amurka Donald Trump ya soke taron da ya shirya yi da takwaransa na Koriya Ta Arewa Kim Jong-un, yana mai cewa taron bai dace a wannan lokacin ba.

Ya ce ya yanke wannan hukunci ne saboda fushi da nuna isar da Koriya Ta Arewa ta yi a wata sanarwarta ta baya-bayan nan.

Mista Trump ya ce bai dace a yi taron ba a wannan lokaci, wanda aka shirya yin sa ranar 12 ga watan Yuni a kasar Singapore.

A wata wasika da ya aike wa Mista Kim, ya ce yana matukar sa ran ganawa da shi "wata rana".

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Tabarbarewar diflomasiyya

Sharhi daga Jonathan Marcus, wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya

Gwamnatin Shugaba Trump ta hakikance cewa Koriya ta Arewa ba ta bayar da hadin kan da ya kamata ba wajen shirye-shiryen ganawar, lamarin da ya sa shakku kan ko ganawar za ta iya samar da sakamakon da ake so.

Babbar tambaya ita ce mene ne zai faru a yanzu?

Kafin a fara samun maslafa tsakanin Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa wadda ta sa aka tsayar da ranar ganawar, an yi ta musayar kalamai tsakanin Pyongyang da Washington lamarin da ke haifar da fargaba mai tsanani game da sulhunta rikici a yankin Koriya.

Shin Koriya za ta sake fara gawaje-gwajen makami ne? Shin za a sake fara musayar zafafan kalamai ne? Ko kuma za a iya samun wata dama ta tabbatar da tattaunawar diflomasiyya?