'Matakin Amurka abin takaici ne' inji Koriya ta Arewa

Shugaba Trump da Kim Jong-un na Koriya ta Arewa
Bayanan hoto,

A ranar 12 ga watan Yuni shugabannin biyu ya kamata su gana

Koriya ta Arewa ta ce a shirye take ta tattuna kai tsaye da Amurka bayan da shugaba Trump, cikin bazata ya janye daga taron kolin da aka shirya yi da shugabanta Kim Jong-un.

Tun da farko, Koriya ta Arewar ta nuna rashin jin dadinta da matakin na shugaba Trump.

Kafar yadda labaran kasar ta ce ba haka aka so ba, domin Mista Kim ya yi iya kokarinsa don ganin tattaunawar ta tabbata.

Sanarwar da mataimakin ministan harkokin wajen Koriyar ya fitar, ta ce har yanzu kasar a shirye ta ke ta tattauna keke da keke da Amurka a cikin kowane hali da lokaci.

Batun da ke zuwa da mamaki ganin cewa ya zo kwana guda da kasar ta bayyana mataimakin shugaban Amurkan Mike Pence a matsayin 'Wawa dakiki.'

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nuna damuwarsa matuka a kan yanayin da ake ciki.

Yayin da shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in ya gayyaci manyan hafsoshin tsaron kasar domin tattaunawa a cikin gaggawa.

Ita kuwa shugabar jam'iyya marasa rinjaye ta Democrats, Nancy Pelosi, ta ce batun Koriya ta Arewa ya wuce karfin tunanin Mista Trump.

A bangaren yarjejeniyar nukiliyar Iran, hukumar da ke sa ido kan makaman nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce Iran na mutunta yarjejeniyar.

Amma duk da haka Mista Trump ya janye kasarsa daga yarjejeniyar ba tare da ya samar da wadda ta fi ta ba.

Bayan nan Shugaban na Amuka ya mayar da hankalinsa kan taron koli tsakaninsa da shugaba Koriya ta Arewa Kim Jong un.

Amma a nan ma shugaban bai iya cimma nasarar da ya so ba.

Masu lura da siyasar Amurka sun ce Shugaba Trump ya janye daga halartar taron ne domin ya tabbata cewa Koriya ta Arewa ta fusata da wasu kalamai da jami'an Amurkar suka furta - musamman na kwatanta kasar da Libya da John Bolton, mai bai wa shugaban Amurkan shawara kan tsaro ya yi.

Masana na ganin cewa shugaba Trump ya nuna gazawarsa, wajen iya mulki da diflomasiyya a daidai lokacin da duniya ke bukatan kwararren jagora.

Sun kuma ce a maimakon shugaba Trump ya bayar da shugabancin da zai warware matsalolin, sai ya gudu ya bar ladansa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da kuma taron koli da Koriya ta Arewa.