An tuhumi mai shirya fina-finai Harvey Weinstein da fyade

An fitar da Weinstein daga kotu bayan an bayar da belinsa
Bayanan hoto,

An fitar da Weinstein daga kotu bayan an bayar da belinsa

An tuhumi mai shirya fina-finan Hollywood din nan da a ka kunyata Harvey Weinstein da laifukan fyade da cin zarafi, bayan da ya mika kansa ga 'yan sanda a birnin New York ranar Juma'a.

A wata sanarwar da rundunar 'yan sandar New York ta fitar ta ce an kama Mr Weinstein tare da tuhumarsa da laifukan da suka jibanci yi wa mata biyu fyade.

Wannan na zuwa ne kusan wata takwas bayan da sana'arsa ta shiga matsala sakamakon zarge-zargen cin zarafin mata da ya fuskanta a masana'antar ta fim.

Lauyansa, Ben Brafman, ya shaida wa 'yan jarida a wajen kotu bayan an bayar da belin Weinstein cewar za su kalubalanci tuhume-tuhumen.

A baya, Mr Weinstein ya shirya fina-finan da suka lashe lambar yabo ta Oscar.

Mai shirya fina-finan mai shekara 66 dai ya kai kansa caji ofis ne a Manhattan inda lauyoyinsa suka mara masa baya.

Bayanan hoto,

Harvey Weinstein ya ce zai kalubalanci zarge-zargen da ake yi masa

A na hasashen cewa an dauki hotonsa da zanen yatsunsa, daga nan kuma a ka wuce da shi wata kotu a Manhattan kuma rahotanni sun ce ya amince zai biya kudin belinsa dala miliyan daya tsaba.

Hakazalika zai sanya wata na'ura a jikinsa da za ta rika sa masa ido. Za a iyakance masa tafiye-tafiye kuma zai sallamar da fasfo din sa.

Ofishin babban lauyan gundumar Manhattan da rundunar 'yan sandan New York sun kwashe tsawon watanni suna bincikar Weinstein, inda ya fuskanci matsin lamba daga masu fafutukar kare hakkin mata masu amfani da maudu'in #Time'sUp don ganin an gurfanar da shi.

Zaman kotun dai na ranar Juma'a shi ne karon farko na zargin miyagun laifuka da ake yi wa tsohon mai shirya finan-finan da a ka kunyata.