Soyayyar Mo Salah ta game kasar Masar

Soyayyar Mo Salah ta game kasar Masar

A hankali, sannu a tashi, Mohamed Salah na ci gaba da kwantawa a zukatan 'yan kasar Masar da wasu masu sha'awar kwallo a sassan duniya daban-daban.

Nasarorin da dan kwallon ya ke samu a Liverpool sun sa tauraruwarsa na ci gaba da haskakawa, abin da ya sa ake kwatanta shi da manyan 'yan kwallo irinsu Ronaldo da Messi.

Sai dai abokanansa da wadanda suka san shi tun asali, sun ce har yanzu dan kwallon bai sauya halinsa na dattaku da sanin darajar mutane ne ba, duk da wannan daukaka da ya samu.