Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon jiya
Wadansu daga cikin hotunan abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka a makon jiya.

Asalin hoton, AFP
Wani mawaki lokacin wani taron raye-raye da wake-wake a birnin al-Khahira na kasar Masar
Asalin hoton, AFP
Raye-rayen suna da farin jini ga al'ummar yankin Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, EPA
Wadansu masu wake-wake daga kasar Syria lokacin wani taron al'adu a birnin Tunis na kasar Tunusiya ranar Talata
Asalin hoton, AFP
Wadansu kayayyakin tarihi na Masarautar Dahomey wadda take cikin kasar Jamhuriyar Benin a yanzu, a wani gidan adana kayan tarihi da ke birnin Paris na kasar Faransa. Benin ta bukaci a mayar mata da kayayyakin tarihin da aka kai Turai lokacin mulkin mallaka.
Asalin hoton, Getty Images
Wani mai sayar da naman daji lokacin da ya rike nama a wata kasuwa a birnin Mbandaka na Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, birnin yana fama da annubar Ebola.
Asalin hoton, AFP
Wata mai fafutikar kare hakkin 'yan luwadi Yvonne Oduor lokacin da take rike da wata tuta a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Nairobi na kasar Kenya
Asalin hoton, AFP
Wani mai goyon bayan Senegal lokacin da yake rike da tutar kasar yayin da yake sauraron sunayen 'yan wasan kasar da za su je Gasar Cin Kofin Duniya wanda za a yi a kasar Rasha
Asalin hoton, Reuters
Wani dan Ghana Joseph Afrane lokacin da ya yi tsayuwar daukar hoto a birnin Windsor a kasar Birtaniya yayin bikin Gidan Sarautar kasar
Asalin hoton, Reuters
Wata mai tallan kayan kawa a otel din Windsor Golf da Country Club a birnin Nairobi na kasar Kenya
Asalin hoton, EPA
Wata 'yar kasar Afirka ta Kudu lokacin da take kallon daurin auren Yarima Harry da Meghan Markle a talabijin a birnin Cape Town ranar Asabar
Asalin hoton, AFP
Wani mutum lokacin da yake karanta wani littafi wanda wani marubuci dan kasar Kwaddibuwa Epiphane Zoro Bi ya rubuta. Littafin yana magana ne game da kabilar yankin Ituri a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, inda fiye da mutum 60,000 suka rasa rayukansu.
Asalin hoton, AFP
Wani mutum lokacin da yake kokarin kubutar da kayansa daga ambaliyar ruwa a birnin Mogadishu na kasar Somaliya
Asalin hoton, Reuters
... wannan mutumin ya shiga ambaliyar ruwa ne da taimakon keken jakinsa don ketara hanya
Asalin hoton, Reuters
Wani yaro lokacin da ya fada cikin ruwa saboda yanayin zafi da ya yi tsanani a birnin Alkhahira na kasar Masar ranar Laraba
Asalin hoton, AFP
Wadansu 'yan Najeriya suna addu'a game da kashe-kashen da ke faruwa a kasar a Legas ranar Talata
Asalin hoton, AFP
Wata mai tallan kayan kawa Miriam Odemba lokacin da ta halarci taron fina-finan na Cannes Film Festival a kudancin kasar Faransa
Hotuna daga AFP, Getty Images, Reuters da kuma EPA