Yadda harin sama na Saudiyya ya kashe masu taron biki

Tun lokacin da aka fara yakin Yemen shekaru hudu da suka gabata, an kashe fiye da mutum 10,000, an kuma raba miliyoyi da gidajensu.

Wakiliyar BBC Nawal Al-Maghafi ta samu wani bidiyo na yadda daya daga cikin hare-haren saman da ake kai wa ya yi sanadin rayuwar wasu.