Jarumtakar da dan ci-rani ya nuna ta sa ya zama dan kasa a Faransa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Lokacin da dan ci-ranin ya ceto yaro a wani bene

An jinjina wa wani dan ci-rani daga kasar Mali sakamakon kwazon da ya nuna wajan hawa wani bene da ke birnin Paris na Faransa, domin ya ceto wani karamin yaro da ya makale kuma yana gab da fadowa daga bene hawa na hudu.

An dai yada hoton bidiyon Mamoudou Gassama a shafukan sada zumunta lokacin da ya kubatar da yaron.

A cikin minti daya ya hau ginin in da ya dauki yaron mai shekara hudu, wanda wani makwabcin iyayen yaron ke rike da hannunsa domin ka da ya fado kasa.

Shugaba Emmaneul Macron na Faransa ya gayyaci Mista Gassama zuwa fadar Elysee a ranar Litinin, domin ya yi masa godiya.

An dai walafa hoton bidiyon ne a shafin Facebook.

Hakkin mallakar hoto Image copyrightREUTERS
Image caption Mr Gassama ya gana da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa a ranar Litinin

Da yammacin ranar Asabar ne al'amarin ya faru a wata unguwa da ke arewacin Paris.

Mista Gassama ya ce yana tafiya ne lokacin da ya ga jama'a sun taru a gaban ginin.

Ya shaida wa kafar watsa labarai ta Faransa watau BFMTC cewa, lokacin da ya ga yaron yana ta shilo a bene, "Ban tsaya yin tunani ba, nan take na yanke shawarar ceto shi."

"Da na rike a shi a hannuna, na yi masa magana kuma na tambayeshi; me yasa ka yi haka? Sai dai be ce min komai ba".

'Yan sanda na yi wa mahaifin yaron tambayoyi bisa zargin cewa ya bar dansa a gida ba tare da kowa ba, a cewar wata majiyar shari'a.

Ana kyautata zaton mahaifiyar yaron ba ta Paris lokacin da al'amarin ya faru.

Magajin garin Paris Anne Hidalgo, ta jingina wa matashin mai shekara 22, kuma ta ce ta kira shi ta waya domin ta yi masa godiya.

Ta kuma ce ya kamata dukkanin 'yan kasar su yi koyi da abin da ya yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gassama ya daga takardar shaiidar girmamawa da aka ba shi bayan ya fito daga fadar shugaban kasa

Labarai masu alaka