'Ya kamata mata su shiga a dama da su a zaben 2019'

'Ya kamata mata su shiga a dama da su a zaben 2019'

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron tattaunawar da Fatima Zahra Umar ta yi da wasu mata kan maudu'in:

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce kashi 44 cikin 100 na masu zaben kasar ne mata. Da alama anyi adalci a wadannan alkalluman. Sai dai kuma idan aka dubi alkalluman jiha-jiha, musamman ma a jihohin arewacin Najeriya, za a ga abin ba haka yake ba.

A shirinmu na wannan makon mun mayar da hankali ne kan wannan matsalar. Kuma mun karfafa muku gwiwa domin ku je ku yi rijista domin ku iya yin zabe tare da saukar da nauyin da ya rataya a kanku a matsayinku na 'yan kasa.