Shugabannin Koriya biyu sun yi ganawar ba-zata

Kim Jong-un and Moon Jae-in meet 26 May

Asalin hoton, The Blue House/Twitter

Shugabannin Koriya ta Arewa da Koriya ta kudu sun gana a kan bakin iyakarsu da ke tsakanin kasashen biyu inda babu soji.

Ganawar ita ce ta biyu tsakanin shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in da kuma na Koriya da Arewa, Kim Jong-un.

Ganarwar ta zo a lokacin da bangarorin biyu suke ci gaba da kokarin ganin sun farfado da ganawar da aka shirya tun da farko tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa mai cike da tarihi.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya soke ganawar, wadda aka shirya yi a Singapore ranar 12 Yuni, amma daga baya ya nuna cewa za a iya ganawar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Moon Jae-in (na biyu daga hagu) tare da Kim Jong-un (ta dama) sun tattauna a bakin iyaka

An yi tattaunawar baya bayan nan ne a arewacin kauyen sulhu na Panmunjom, tsakanin karfe uku zuwa karfe biyar na yankin, in ji ofishin Mista Moon