Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun gana kan Buhari

Bukola Saraki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanata Bukola Saraki shi ne jami'in gwamnati mafi girma da ya halarci taron

Tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun yi taro kan makomarsu a jam'iyyar APC.

Wata sanarwa da Alhaji Abubakar Kawu Baraje, shugaban 'yan PDP sabuwa ya raba wa manema labarai ta ce taron ya biyo bayan wasikar koken da 'yan siyasar suka rubuta wa jam'iyyar APC mai mulki ne da kuma ganawar da shugabanninsu suka yi da jam'iyyar APC bayan wasikar.

Shugaban majalisar wakilan, ya ce a taron da aka yi domin sanar da 'yan sabuwar PDP din abin da jam'iyyar APC ta sanar da wakilan sabuwar PDP din, an kafa kwamiti daban daban.

Shugabannin majalisar dokokin Najeriyasun halarci taron wanda ka iya tasiri kan makomar jam'iyyar APC mai mulki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugabannin majalisar dokokin Najeriya sun halarci taron wanda ka iya tasiri kan makomar jam'iyyar APC mai mulki

Ya ce muhimmin makasudin kafa kwamitin shi ne ta yadda za a ceto Najeriya daga kalubale na siyasa da zamantakewa da kuma na tsaro.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Prince Olagunsoye Oyinlola da Admiral Murtala Nyako (Rtd) da kuma Sanata Mohammad Adamu Aliero.

Akwai Sanata Danjuma Goje da Sanata John Owan Enoh da Sanata Emmanuel Andy Uba da Sanata Ibrahim Gobir da Sanata Rufai Ibrahim da Sanata Ibrahim A. Danbaba da Sanata Suleman Nazif da kuma Sanata Isa Hamma Misau.

Akwai kuma Sanata Muhammed Ubali Shitu da Sanata Shehu Sani da Sanata Dino Melaye da Sanata Suleiman O. Hunkuyi da Sanata Shaaba Lafiagi da Sanata Bala Ibn Na'Allah da Sanata David Umaru

Sauran sun hada da Sanata Barnabas Gemade da kuma Alhaji Abubakar K. Baraje wanda shi ne tsohon shugaban sabuwar PDP din.

Sanarwar dai ba ta ambaci wani mataki da 'yan siyasar ke son dauka kan Shugaba Buhari ko kuma jam'iyyarsa ta APC ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sanarwar dai ba ta ambaci wani mataki da 'yan siyasar ke son dauka kan Shugaba Buhari ko kuma jam'iyyarsa ta APC ba

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Aminu Shagari da Kabiru Marafa Achida da Isa M. Ashiru da Muh'd Musa Soba da Mark Gbillah da Sani Mohd Rano da Garba Umar Durbunde da Aliyu Madaki da Zakari Mohammed.

Akwai kuma Rufai Ahmed Chachangi da Razak Atunwa da Emmanuel M. Udende da Hassan Saleh da Nasiru Garo Sule da kuma Orker Jev.

Sauran 'yan majlisar da suka halarci taron su ne Aliyu Ahman Pategi da Isah Halilu B. da Rabiu Garba Kaugama da Abdussamad Dasuki da Ismaila A. Gadaka da Lado Suleja da Dickson Tarkighir da Babatunde Kolawole da Bode Ayorinde da U. Danjuma Shida da Danburam Nuhu da Sunday Adepoju da Sani Zorro da Ahmed Garba Bichi da Garba Ibrahim Mohammed da sauransu.

Sai dai kuma a cikin wadanda sanarwar ta ce sun halarci taron akwai wadanda ba su cikin 'yan sabuwar PDP din da suka hade da jam'iyyar APC gabannin zaben 2015.