Ba zan taba daina kewar matata Sridevi ba — Boney Kapoor

Boney Kapoor da matarsa marigayiya Sridevi Hakkin mallakar hoto Hindustan Times
Image caption Boney Kapoor da matarsa marigayiya Sridevi

Mjin jaruma Sridevi wadda ta rasu watanni uku da suka wuce, wato Boney Kapoor, ya bayyana yadda yake rayuwa bayan rasuwar matarsa.

Boney Kapoor, wanda mai shirya fina-finai ne wato furodusa, ya ce shi yanzu yana kokari ne ya ga ya zame wa 'ya'yansa biyu da suka Haifa da Sridevi uwa da uba.

Boney ya ce ' Har yanzu ina matukar alhini da kewar matata Sridevi, saboda yadda muke matukar kaunar juna tun da muka yi aure, rashinta ba karamin babban gibi bane a gare ni da kuma yaranmu biyu, wato Jhanvi da Khushi Kapoor'.

Ya ce ' Matata Sridevi, babbar Katanga ce a gareni, akwai abubuwa da dama da ta fara, yanzu komai ya tsaya cak, amma kuma ina kokari naga na ci gaba da tafiyar da al'mura yadda yakamata'.

Boney Kapoor wanda yayane ga jarumi Anil Kapoor da kuma Sanjay Kapoor, yace saboda yaransa yake kokari yaga ya ci gaba da tafiyar da rayuwarsa yadda ya kamata.

Yawanci duk inda 'ya'yan nasu za su je, a kan gansu tare da babansu, musamman babbar 'yar su tare da Sridevi, Jhanvi, wani lokaci a kan ganshi ya rike hannun yaran nasa, kamar kanana, kuma duk yana hakan ne domin cike gibin mahaifiyarsu da suka rasa wadda a duk inda suke tare ake ganinsu.

Boney Kapoor, yace ' Jina na ke kamar fanko, saboda rashin matata abar kaunata Sridevi'.

Jaruma Sridevi, ta rasu ne a ranar 25 ga watan Aprilun, 2018 a Dubai.

Wasu majiyoyi sun shaida wa kafafen watsa labarai cewa an gano ta a cikin wurin wankan otal din da suka sauka ba ta motsi.

Rasuwar jarumar ta girgiza masana'antar fina-finai ta Bollywood da ma miliyoyin magoya bayanta da ke sassan duniya baki daya.

Tarihin rayuwar Sridevi

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY

An dai haifi Sridevi ne a ranar 13 ga watan Augustan shekarar 1963 a Tamil Nadu.

Sridevi ta fara fitowa a fina-finan Tamil ne tun tana karama wato tana da shekara hudu a duniya , amma a shekarar 1975 ne ta fito a fim da girmanta wato fim din Julie, daga nan ne ta ci gaba da fitowa a fina-finai amma na Tamil.

Fim dinta na farko da ta yi wato na Hindi shi ne fim din Solva Sawan wanda aka yi shi a shekarar 1979.

Shekara hudu bayan nan kuma sai aka hadata fim da Jeetandra wato fim din Himmatwala wanda kuma ya yi matukar fice a shekarar da aka sake shi wato 1983.

Daga nan ne fa Sridevi ta koma fitowa a fina-finan Hindi.

Tayi fina-finai fiye da 150 ciki har da wadanda da suka yi fice kamar, Mawali da Sadma da Mr India da Chandni da Nagina da Chalbaaz da Janbaaz da English Vinglish da Chandra Mukhi da kuma fim din ta na karshe da ya fita bara wato Mom.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya mata biyu wato Jhanvi da Khushi Kapoor.

Sridevi ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa a fina-finan Bollywood.

Ta karbi lambobin yabo da dama bisa rawar da ta taka a fina-finan.

Tana daga cikin jarumai mata da suke da kyau sosai, da kuma iya rawa.

Ta fara auren jarumi Mithun Jakraborty ba su haihu ba, daga baya kuma ta auri mai shirya fim da bayar da umarni Boney Kapoor, inda suka haifi 'ya'ya biyu mata Jhanvi da Khushi Kapoor.

Labarai masu alaka