'Adalci ne kadai zai warware matsalar yajin aiki a Nigeria'

Ma'aikatan lafiya na ci gaba da yajin aiki a Najeriya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikatan lafiya na ci gaba da yajin aiki a Najeriya.

Kungiyar Kwadago a Najeriya, wato NLC, ta bayyana damuwa kan yadda harkar kiwon lafiya ke kara tabarbarewa a sakamakon yajin aikin ma'aikatan kiwon lafiya a kasar.

Kungiyar ma'aikatan ta shafe makonni da dama tana yajin aiki na sai abin-da-hali ya yi a yunkurin neman wasu bukatu na ta daga gwamnatin tarayya.

Cikin wata hira da BBC Hausa, shugaban kungiyar kwadagon Kwamared Ayuba Wabba, ya ce ba a bi hanyoyin da suka dace wajen warware matsalar ba.

A cewarsa, an samu matsaloli ne wajen aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma ne tsakanin kungiyoyin masu aikin kiwon lafiya da na gwamnati a shekarun baya.

Kwamared Wabba ya ce 'An yi wa wasu bangarori na ma'aikatan kiwon lafiya karin albashi, ba tare da an yi wa wani bangare kari ba, kuma sun koka sau da dama kafin wannan lokaci da ake ciki yanzu.'

Wabba ya kara da cewa ministan lafiya na Najeriya na daga cikin wadanda suka dagula kokarin kawo maslaha a kan rikicin, a saboda haka ne kungiyar kwadagon ke kokarin ganin an kawo mutane na daban wadanda za su tattauna kan yadda za a shawo kan matsalar.

Adalci ne kadai zai sa a warware matsalar, in ji Wabba.

Ya ce ' Tunda an yi wa bangare daya kari (albashi), dole ne dayen bangaren ma a duba yadda za a yi masa karin sai a samu zaman lafiya da fahimtar juna.'

Labarai masu alaka