Buhari da APC na yi wa damokuradiya zagon kasa - PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta ce babu wani amfani da bikin zagayowar ranar damokradiya zai yi wa 'yan kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, PDP, ta ce, babu wani abu da 'yan Najeriya ke gani a cikin wannan mulki bayan take hakin dan adam.

Mataimaki na musamman a jam'iyar ta PDP a bangaren watsa labarai, Shehu Yussuf Kura, ya shaida wa BBC cewa, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki wani mataki na habaka damokradiya ba a kasar, illa ma takura ta da yi mata zagon kasa.

Kawo yanzu gwamnatin da kuma jam'iyyar APC ba su ce komai game da wadannan kalamai na PDP.

A ranar Talata ne kasar ke cika shekara 19 da komawa kan tafarkin damokuradiya.