Shan kwaya ya sa za a rusa unguwar Galadima da ke Maiduguri

Shan kayan maye babbar matsala ce a Najeriya
Bayanan hoto,

Shan kayan maye babbar matsala ce a Najeriya

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta sanar da aniyarta ta rusa unguwar Galadima wadda ke Maiduguri, babban birnin jihar, saboda yawan shan kwaya da ake yi.

Jihar ce ta fi kowacce jiha a Najeriya shan wahala a kan rikicin kungiyar Boko Haram, wadda ake zargi da kashe dubban mutane tare da tarwatsa miliyoyin al'umma a yankin arewa-maso-gabashin kasar da kuma kasashe masu makwaftaka.

Gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin rusa unguwar Galadima sakamakon kaurin sunan da unguwar ta yi wajen shan miyagun kwayoyi.

A hirarsa da BBC, babban mai taimaka wa gwamnan jihar na musamman kan harkokin yada labarai, Mallam Usman Maji Dadi Kumo, ya ce unguwar ta yi kaurin suna wajen shan kwaya, da tabar wiwi, da kodin da duk wani abin da ke sa maye.

Ya ce shaye-shayen da ake yi a unguwar sun munana, kuma gwamnati ba za ta bar duk wani abu da ke da hadarin sake kawo tashin hankali a jihar ba.

A cewarsa, wutar da ta kone jihar, ba za a bari ta sake kamawa ba.

A saboda haka ya ce za a rushe ilahirin unguwar bayan an biya dukkanin wadanda suka mallaki filaye bisa ka'ida a unguwar diyya.

A kwanakin baya ma gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe wasu kamfanonin hada magunguna bayan da aka zarge su da laifin sayar da wasu magunguna ba bisa ka'ida ba, wadanda ake amfani da su wajen yin maye.

To sai dai kuma wasu na fargabar wannan mataki na gwamnatin Borno ya yi tsauri musamman bisa la'akari da yadda jihar ke fama da matsalar 'yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram.

Amma gwamnatin jihar ta bakin Mallam Usman Maji Dadi Kumo, ya ce dama unguwar ta Galadima tun asali filin jirgin kasa ne, mutane suka mayar da ita mashaya.

Ya ce ba wai unguwa ce da ta ke tarin gidaje ba, akwai dai kantuna da otel-otel, sai kuma dai-daikun gidaje.

A baya dai kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi dakarun Najeriya masu aikin samar da zaman lafiya a yankin da Boko Haram ta addaba da laifin cin zarafin bil'adama, zargin da hukumomin kasar suka musanta.