Amurka da Rwanda na fada kan kayan gwanjo

Wani mai sayar da kayan gwanjo a Kenya a ranar 25 ga watan Yuni , 2012, a Nairobi. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai sayar da kayan gwanjo

Matakin farko da Shugaba Donald Trump na Amurka ya dauka kan cinikayyar kasashen duniya ya shafi Rwanda, inda ya sanya kudin fito a kan kayayyakin da ake shigo wa da su daga kasar wacce ke gabashin Afrika.

Matakin yana da nasaba da kayan gwanjon da ake kai wa kasar da kuma matsayin da Rwanda ta dauka na kin sauya shawara kan wata takaddama da ta kunno kai.

Yaushe ne takaddamar ta kuno kai?

Watan Maris na shekarar 2018 shi ne wa'adin kwanakin 60 da Amurka ta dibar wa Rwanda, a kan cewa za ta dakatar da kasar wadda ba ta da teku, daga sayar da kayayaki a kasuwar da ba a dorawa haraji, wanda matsayi ne da ta ke cin gajiyarsa karkashin shirin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka wato Agoa.

Agoa wani shirin kasuwanci ne na Amurka da aka tsara domin bunkasa kasuwanci da zuba jari a kasashen Afrika da suka cancanta ta hanyar ba su damar shigo da kayayaki 6.500 ba tare da an biya haraji ba.

"Shugaban kasa ba shi da aniyar aiwatar da dokar da kuma tabbatar da adalci a dangantakar kasuwanci da ke tsakaninmu,"in ji mataimakin wakilin kasuwanci na Amurka, CJ Mahoney.

A yanzu wa'adin kwanaki 60 ya zo karshe.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babu fara'a a fuskar Donald Trump da Paul Kagame a ganawar da suka yi a watan Janairu

Shin me yasa Rwanda ta hana shigar da kayan gwanjo cikin kasar?

Manufar gwamnatin kasar ita ce ta kare bangaren kamfanonin masakun kasar.

Akwai wasu kasashen Afirka wadanda a baya masakunsu sun yi tasiri sosai. Sai dai rashin shugabanci nagari da almundahana da kuma karuwar gogaya tsakanin kasashen duniya ta sa bangaren ya durkushe.

Wannan ya faru a kasar Ghana inda wani bincike da aka yi ya gano matakin da gwamnatin ta dauka na cire hannunta daga masaku a shekarun 1980 ya sa bangaren ya fuskanci koma baya matuka, inda yawan ma'aikata da ke aiki a masaku ya ragu daga 25,000 a shekarar 1977 zuwa 5,000 a shekarar 2000.

Haka al'amarin yake a Kenya inda a baya mutane 500,000 ne suke aiki a masakun kasar , amma yanzu adadin da suka rage be taka kara ya karya ba.

Kayan gwanjo na cikin abubuwan da suka janyo dukushewar masaku a kasashen kudu da sahara na Afrika.

Tufafin da aka turowa daga kasashen yamma sun kasance masu farashi mai rahusa , abinda kuma ya sa masana'antu da kuma teloli su ka kasa gogaya da su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai kasuwannin gwanjo irin ta Gikomba da ke Nairobi a kasashen Afirka daban-daban

Gwamnatocin kasashen Afirka sun yi korafin cewa yawan bukatar da ake yi wa kayan da aka yi a cikin gida na fuskantar koma baya saboda a farashi mai rahusa ake sayar da kayan gwanjon.

A shekarar 2015 kasashen suka yi shelar hana sayar da kayan gwanjo a kasuwani kuma matakin zai fara aiki ne a shekarar 2019.

Gwamnatin Rwanda ta ce kayan gwanjo na kawo barazana ga martabar al'ummarta.

Rwanda ta kara kudin haraji kan kayayakin da ake shigo wa da su daga waje a shekarar 2016.

Manufar tsarin shi ne a kawarda da sauran kayan gwanjo da suka rage a cikin kasuwa.

Fatan gwamnatin Rwanda shi ne matakin zai taimaka wajen farfado da bangaren masakun kasar kuma zai samar da guraben ayyuka fiye da 25,000.

Me yasa Amurka ta fusata?

Al'amarin ya samo asali ne lokacin da wata kungiyar kasuwanci a Amurka ta shigar da koke a gaban ofishin cinikayya na kasar.

Kungiyar da ake kira SMRTA ta ce matakin da kasashen gabashin Afirka suka dauka a shekaar 2015 hana shigo da kayan gwanjo zai shafi bangaren masakun Amurka.

An yi kiyasin cewa haramcin shigo da kayan gwanjo zai sa ma'aikata 40,000 su rasa ayyukansu a Amurka da kuma dala miliyan 124.

Sai dai wasu sun ce akwai alamar tambaya kan alkaluman.

"Kasashen gabashin Afirka sun nuna shaku kan alkaluman na kungiyar SMRTA" Grant T Harris, mai ba tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama shawara kan batutuwan da suka shafi Afirka ya shaida wa BBC.

A watan Maris na shekarar bara ne Amurka ta yi barazanar cire kasashen Kenya da Uganda da Tanzaniya da Rwanda daga cikin shirin Agoa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fatan Rwanda shi ne ta koma kasa mai masakaicin karfi kafin 2020

Shin ko Amurka ta yi adalci a matakin da ta dauka ?

A wani bangare za a iya cewa eh, a wani bangaren kuma a'a .Amurka na da hakki ta bukaci kasashe su kawarda da duk wani shinge karkashin shirin Agoa kuma wannan shi ne manufarta.

"Sai dai ba wai yana nufin ta yi dai-dai da ta dauki wannan mataki ba," in ji Mr Harris." Manufar Agoa ita ce a yi amfani da kasuwanci wajen kawo ci gaba da bunkasar tattalin arziki."

Ya kuma kara da cewa Amurka ta bude kofofinta ga kayayakin da aka yi a wasu kasashe ba tare da haraji ba wandanda suka kafa shinge a kan wasu kayayakin da ake shigowa da da su daga Amurka irinsu Indiya da Brazil

" Matakin zai fi yin tasiri idan Amurka ta dauki matsayin ba sani ba sabo a kan kowace kasa wadda ta hana shigo kayayayinta .

Ya ce mafi alheri shi ne Amurka da Rwanda su zauna a kan teburin shawara ba tare da gwamnatin kasar ta yi amfani da shiri Agoa domin cimma burinta .

Shin ta ya ya matakin zai shafi Rwanda?

Duk da cewa Amurka ba ita ce kasar da Rwanda ta fi fitar da kayayyakinta ba amma matakin zai iya shafar kasar.

Florie Liser, tsohuwar mai taimakawa wakilin Amurka kan harkokin kasuwanci a Afirka ta shaida wa BBC.

"Akwai ayyukan da za su shiga cikin hadari kuma haraji watakila ya bai wa masu zuba jari da suke son su rika cin karensu ba bu babbaka karkashin shirin na Agoa tsoro", in ji ta.

Image caption An yi kiyasin cewa ana samun dala miliyan 20 daga harkar sayar da kayan gwanjo

Sai dai shugaba Paul Kagame na Rwanda ya nuna cewa a shirye ya ke ya sadaukar da kasar domin tattalin arzikinta ya bunkasa.

"Wannan shi ne matakin da mu ke ganin ya dace. A gani na wannan zabi shi ne ma fi sauki duk da cewa watakila za mu wahala," in ji shi a 2017.

"Rwanda da sauran kasashen yankin da ke cikin shirin Agoa, na bukatar yin wasu abubuwa - ya kamata mu raya kuma mu kafa masana'antunmu."

Sai dai kwararru sun ce kasar da za ta samu galaba a wannan takaddama ita ce China.

A cewar wani bincike na kungiyar samar da cigaban rayuwa ta Amurka wato USAID China na shigo da tufafi zuwa gabashin Afirka a cikin farashi mai rahusa da aka yi kiyasin cewa ya kai dala biliyan daya.

Wannan ya kuma sa akwai rata sosai a darajar gwanjo da ake shigo da su daga kasashen waje - wanda kashi 40 cikin 100 na talakawa a gabashin Afirka ke saya.