Hotunan yadda leda ke sa duniya cikin matsala

A cikin rahotonta na watan Yuni, mujallar kafar watsa labarai kan al'amuran da suka shafi dabbobi da muhalli, ta wallafa wasu zababbun hotuna masu ban mamaki da ke nuna yawan bolar da ke yashe a cikin tekuna da koguna.

Namun daji, musamman dabbobin ruwa, suna cikin hadari a duk lokacin da suka ci karo da tarkacen bola ko ledoji ko roba, ko kuma idan suka hadiya.

Hakkin mallakar hoto NAtional Geographic

Wannan tsuntsun da aka fi sani da zalbe ya ci sa'a da ya samu ya tsira, bayan da ya makale a cikin leda a gabar teku a Spain- mai daukar hoton ne ya cire masa ledar daga baya.

Leda daya na iya kisa fiye da sau daya. Mushe na rubewa, amma roba tana dadewa.

Hakkin mallakar hoto Jordi Chias / NAtional Geographic

Wannan kunkurun ya makale a cikin wani tsohon komo na roba a tekun Mediterranean kusa da gabar tekun kasar Spain.

Kunkurun na iya mika wuyansa har saman ruwa don samun numfashi amma ba don mai daukar hoton ya warware shi ba da ya mutu.

Kayan kamun kifin da aka yi watsi da su babbar barazana ce ga dabbobin ruwa irin su kunkurun ruwa.

Hakkin mallakar hoto SHAWNMILLER2014

A gabar tekun Okinawa na kasar Japan, wata kaguwa ta shige cikin murfin kwalbar roba don bai wa tumbinta karuya. yi amfani da kwalbar roba don kare kugunsa mai taushi.

Masu zuwa gabar teku suna debo kokon bayan kaguwar, yayin da suke barin dattinsu a baya.

Hakkin mallakar hoto NAtional Geographic

Mujallar ta tattuna batun matsalar sosai; gurbin roba da muke iya gani a farfajiyar, mai yiwuwa kadan ne kawai daga abin da yake cikin teku.

Robobi da ledoji na iya farfashewa zuwa kananun kwayoyi, wadanda ba a iya gani sosai, amma duk da haka suna iya cutar da dabbobin ruwa.

Hakkin mallakar hoto Randy Olson

Wata mata a Bangledash ta baza ledodji don su bushe, bayan da igiyar ruwa ta kwaso dattin leda da roba daga cikin Kogin Buriganga da ke babban birnin kasar Dhaka.

Ta na juya su a kai a kai, yayin da kuma take kula da danta.

Karshen ta a sayar da ledojin ga masu sabuntawa. Kasa da kashi daya cikin biyar kawai na ledoji ake ake sabuntawa a duniya. A Amurka kuwa ana sabunta kasa da kashi 10 cikin 100

Hakkin mallakar hoto Brian Lehmann / National Geographic

Wadannan Kurayen suna kale ne a wani rami da ake zuba shara a birnin Harar na kasar Habasha.

Sun saba da sabuwar hanyar samun abincinsu: dabbobin su kan jira manyan motocin da ke jibge shara a bolar, sai su yi ta dubawa don samun abinci a cikin sharar.

Hakkin mallakar hoto Randy Olson / NAtional Geographic

Mabubbugar ruwa ta Cibeles da ke tsakiyar birnin Madrid ta cika makil da kwalaben roba.

Wata kungiyar masu zane-zane da ake kira Luzinterruptus ce ta cika wannan mabubbugar ruwa da ma wasu guda biyu a birnin, ta hanyar zuba yasassun kwalaben robar 60,000 da nufin jawo hankali ga illar robobi ga muhalli.

Hakkin mallakar hoto Justin Hofman / National Geographic

Don su samu damar tafiya a kan igiyar ruwa, dawakan ruwa kan makale a jikin ciyawar teku da sauran baraguzan da ke yawo a kan ruwan.

A nan wani dokin ruwa ne a wani gurbataccen ruwa da ke tsibirin Sumbawa na kasar Indonesiya ya makale a jikin wani kwanson audugar roba.

Wanda ya dauki hoton Justin Hofman, ya ce "wannan hoto ne da na yi fatan ina ma babu shi".


Ellen MacArthur ce Bakuwar Editar mujallar National Geographic ta watan Yuni.

Wasu fitattun manyan mutane a Birtaniya su 12, wadanda ko wannensu ya yi fice a bangarensa, suna nazari a kan batutuwan da suka hada da ci gaba mai dorewa, kimiyya, kare muhalli, da kuma basirar dan-Adam, tare da hadin gwiwar Babbar Editar Duniya ta mujallar SusanGoldberg da tawagar editocinta.

Wannan wani bangare ne na tsarin Bakon Edita na mujallar a karo na farko.

Labarai masu alaka