Mile 12: Kasuwar da ke hada 'yan Afirka wuri guda

Ana samun kayan gwari na Africa a kasuwar
Image caption Ana sayar da kayan gwari kamar tumatir da tattasai da dankali da albasa wanda ake shigo da su daga arewacin Najeriya da kuma wadansu kasashen Afirka

Babbar kasuwar Mile 12 ta kasance daya daga cikin ma fi girma da ake hada-hadar kayayyakin gwari a tsakanin 'yan kasuwa a nahiyar Afirka.

Kananan 'yan kasuwa daga nahiyar dai kan shigo da kayayyakin gwari da kuma saya bayan fahimtar yanayin farashi da darajar wannan abinci a tsakankanin kasashen.

Mutane na rububin zuwa kasuwar domin samumn saukin farashin kayayyakin gwari.

Da zarar ka shigo kasuwar abin da za ka fara karo da shi shi ne cunkoson mutane - kowa yana harkar gabansa.

Fiye da matasa dubu uku ne ke cin abinci ta hanyar yin dako domin sauke ko daukar kayayyaki da ake shirin fita ko shigowa da su kasuwar Mile 12.

Matasa galibi da su ka fito daga sassan Najeriya daban-daban kan bukaci nuna mu su hanyar kasuwar Mile 12 , kuma fatarsu su fara sana'a kome kankantarta.

Kusan za a ce in akwai wani waje da manoma kan huce takaicinsu bayan tsawon lokaci su na noma to wannan kasuwa mabudi ce a gare su.

Malam Ahmad Musa mataimakin shugaban kananan 'yan kasuwa ne masu sayar da tumatir ya ce "ana yi da kai ya fi ba a yi da kai."

Me ya sa mutane su kan zabi zuwa kasuwar gwari ta Mile 12?

Kayayyakin gwari dai na da daraja sai dai kuma tsadarsu ta sa ma'abuta sayansu kan yi takatsantsan da duba farashi.

Mista Abba Jonathan ya ce samun saukin farashi ne ya sa ya zabi zuwa kasuwar Mile12.

Image caption Dubban matasa ne da suka fiito daga kasashen nahiyar Afirka suke zuwa kasuwar don yin leburanci

"Dalilin da ya sa na zabi sayan kayayyakin gwari a nan shi ne saboda yadda kayayyakin da mu ke saya a kan tituna da sauran wurare suna da tsada. Kayayyakin sun fi sauki a nan."

Kasuwa ce da ta shahara a nahiyar Afirka, bisa la'akari da yadda makwabtan kasashe kan shigo domin saye da sayarwa.

Malami Abdullahi ya shafe fiye da shekara 16 ya na sana'a a wannan kasuwa, ya ce "arzikin noma da Najeriya take da shi, shi ya kawo mata da nasarar kasuwancin kayan gwari."

Malama Fatima 'yar kasuwa ce da ta fito daga Jamhuriyar Benin - ta kan sayi kayyayki domin ketarawa da su zuwa can.

"Na zo kasuwar Mile 12 domin sayan karas da dankali da kabeji domin shiga da su Jamhuriyar Benin. Muna samun saukin kayayyakin a nan. Ina sayar du su ne a kasata."

Shi kuma Abdulkarin Fagbunwo ya shigo da tumatir kasuwar ne daga Jamhuriyar Benin.

Ya ce "Ina shigo da tumatiri zuwa kasuwar Mile 12. Ina karantar yanayin da kasuwar take ciki ne. Misali tumatirin da ake shigo da shi daga arewacin Najeriya ya yi karanci a kasuwar nan, sai na yi sauri na shigo da na mu daga Jamhuriyar Benin."

"Ya ce kowa da ka ga ni a nan na harkokin kasuwancinsa ba tare da damuwa ba. Suna harkokinsu cikin kwanciyar hankali kuma kasuwar tana kai mu su."

Labarai masu alaka