Ko kun san jaruman Indiya da suka yi Hajj da Umrah?

Aamir Khan

Hakkin mallakar hoto Youtube
Image caption Aamir Khan

Jarumi Aamir Khan na daga cikin jaruman fina-finan Indiya da suka samu damar sauke faralli, wato aikin Hajj.

Aamir Khan dai ya sauke faralli ne a shekarar 2012 tare da mahaifiyarsa Zainat Hussain.

Aamir Khan dai ya jima da yi wa mahaifiyarsa alkawarin cewa za su kai ta Makka ta sauke faralli, to hakan ya sa ya cika alkawarin da ya dauka, suka tafi tare suka sauke faralli.

Don haka a iya kiran Aamir Khan da Alhaji a hausance ke nan.

Aamir Khan dai fitaccen jarumi ne da ya fito a manyan fina-finan Indiya da suka shahara ciki har da Laagan da 3 Idiots da Ghajini da kuma Tare Zameen Par.

AR Rehman

Hakkin mallakar hoto The Islamic Information

AR Rehman, fitaccen mawaki ne kuma mai kida a fina-finan Bollywood.

AR Rehman ya yi aikin Hajj har sau biyu, na farko a shekarar 2004, sannan bayan shekara biyu kuma wato a 2006, ya sake komawa.

AR Rehman, a cikin wata hira da ya yi da manema labarai a Indiya, ya ce yana mai matukar alfahari da kasancewarsa Alhaji.

Ya ce ya cika babban burin rayuwarsa da ya ziyarci kasa mai tsarki inda ya yi Umrah da aikin Hajj.

Wasu daga cikin wakokin da AR Rehman ya yi akwai Maa Tujhe Salam da wakar Muqabla da kuma wakar Dil Se Re.

Kader Khan

Hakkin mallakar hoto Ummid

Kader Khan tsohon jarumin fina-finan Indiya ne da ya shahara wajen barkwanci.

Ya fito a fina-finai sama da 300.

Ya fara fitowa a fim ne a shekarar 1973 a fim din Daag.

Mafi yawancin fina-finansa na barkwanci ne. Kader Khan ya kan rubuta labarin fim ma.

Daga cikin fina-finan da ya fito akwai Judaai da Hero No. 1 da kuma Judwaa.

A shekarar 2014 ne Kader Khan ya yi aikin Hajj tare da 'ya'yansa maza biyu wato Shahnawaz da Sarfaraz.

Dilip Kumar

Hakkin mallakar hoto Express

Dattijon jarumi, wanda har yanzu ba a yi kamarsa a Bollywood ba.

Cikakken sunansa Muhammed Yusuf Khan, yanzu yana da sama da shekara sama da 90 a duniya.

Shi ne jarumin da ya fi duk jarumai maza na Indiya samun lambobin yabo.

Ya taka muhimmiyar rawa a Bollywood.

Ba jarumi kadai ba, ya kan rubuta labarin fim, kuma mai fafutuka ne.

Shima ya sauke faralli, amma sai da ya fara zuwa Umrah a 2013, da shekara ta zagayo wato a 2014, sai suka tafi aikin Hajj tare da matarsa Saira Banu.

Daga cikin fina-finan Dilip Kumar akwai Gunga Jumna da Kranti da Saudagar da kuma Mashaal.

Muhammad Rafi

Hakkin mallakar hoto Hamara Photos

A wannan hoto Mohammad Rafi, shi ne a tsakiya. Fitaccen mawaki ne a Indiya.

Ya yi wakoki sama da dubu 28 daga tsakanin shekarar 1944 zuwa 1980.

Daga cikin wakokinsa da suka yi fice akwai wakar Kya Hua Tera Wada da Mere Mehboob Tujhe Salam da kuma Dard-e-dil dard-e-jigar.

A shekarar 1970 ne ya yi aikin Hajj tare da matarsa Bilkis Rafi da kuma dan uwansa Muhammad Din.

Ya rasu a shekarar 1980.

Sana Khan

Hakkin mallakar hoto Instagram

Jaruma ce da ta fi fitowa a fina-finan kudancin indiya. Amma ta fito a wasu fina-finan na Mumbai kamar fim din Toilet ek tha da Jai ho.

A shekarar 2017 ne ta je aikin Hajj.

Labarai masu alaka