An samu raguwar masu shan taba sigari a Faransa

Taba sigari na sanadiyyar mutuwar mutum daya cikin goma Hakkin mallakar hoto Spencer Platt
Image caption Taba sigari na sanadiyyar mutuwar mutum daya cikin goma

Wani kiyasi ya nuna cewa an samu raguwar masu shan taba sigarin a kowace rana, inda aka gane cewa an samu raguwa daga yawan masu shan sigarin tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 a Fraansa.

Bangaren kiwon lafiyar al'umma na kasara ta Faransa, wanda ya gudanar da binciken, ya ce an dade ba a samu sakamako irin haka ba.

Haka nan kuma an samu raguwar zukar tabar a tsakanin matasa, da kuma masu karamin karfi.

Binciken ya ce, yana iya yi wuwa matakan da ake dauka na rage shan sigari a kasar ne suka haifar da raguwar.

A shekarun baya-bayan nan an rinka mayar wa wadanda suka zabi yin amfani da wasu abubuwan na daban baya ga sigari kudadensu, tare da tsawwala kudin sayen taba, da kuma yekuwa a wata-wata kan daina shan taba sigari.

Shan taba sigari na sanadiyyar rasa ran mutum guda a cikin 10.

Yadda kasar Austria ke hana shan Sigari

Wani bincike da aka yi a shekarar 2017, ya nuna cewa kashi 26.9 cikin 100 na masu shekara 18 zuwa 75, na shan taba sigari a kowace rana, idan aka kwatanta da kashi 29.4 cikin 100 da aka gano suna shan sigari din a shekarar 2016.

Hakan ya sanya an samu raguwar masu shan sigari daga mutum miliyan 13.2 zuwa miliyan 12.2 a tsawon lokacin.

Ministar lafiya ta Faransa Agnes Buzyn, ta yi maraba da raguwar yawan masu zukar sigari, musamman tsakanin masu karamin karfi, inda ta ce, al'amarin na matukar cutar da masu rauni a cikin al'umma.

A fadin duniya fa?

Wani nazari da aka gudanar a bara, ya nuna cewa duk da shekarun da aka kwashe ana samar da tsare-tsare na rage shan sigari, sai da aka samu karuwar yawan masu shan sigarin.

Sigari na sanadiyyar rasa rai guda cikin mutum 10 a duniya, kuma rabin irin wadannan mutane na fitowa ne daga kasashe hudu, wato China da India da Amurka da kuma Rasha.

Wani kiyasi ya nuna cewa dabi'ar shan taba sigari na shiga kasashe matsakaita da kuma masu karamin karfi ne daga manyan kasashen duniya.

Hukumar lafiya ta Duniya, na gargadin mutane kan shan sigari ta hanyar amfani da hotuna, kuma ta ce hakan na taimakawa sosai wajen sanya wasu su daina.

Hukumar ta ce, kasashe 78 na duniya na daukar matakan da suka fi dacewa wajen rage masu shan taba sigari.

Labarai masu alaka