Zaben 2019 sai ya fi na 2015 nagarta — INEC

Shugaban hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption Shugaban hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar zaben Najeriya, ta ce ya kamata al'ummar kasar su kwantar da hankulansu a kan batun zaben 2019 da ke karatowa.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Aliyu Bello, ya shaida wa BBC cewa, zaben 2019 sai yafi na 2015 inganci da nagarta da kuma dukkan matakan da ya kamata abi.

Malam Aliyu, ya ce a zaben 2019, ba wanda zai kai ga nasara sai wanda al'umma suka zaba, da kuma wanda kuri'a ta zaba.

"Tanadin hukumar zabe a kullum shi ne a tabbatar da sahihin zabe a 2019," in ji shi.

Ya kara da cewa, daga cikin matakan tabbatar da sahihin zabe a 2019, shi ne tuni aka fara bayar da rijistar zabe ga wadanda ba su da ita, ko kuma wadanda suke da ta wuccin gadi.

Kakakin na INEC ya musanta zargin da wasu 'yan kasar ke yi kan cewa hukumar na shirin kirkirar haramtattun rumfunan zabe har 30,000 da nufin tafka magudi a zaben 2019.

"Shugaban hukumar zabe ya tabbatar da cewa, daga yanzu har zuwa lokacin zaben, babu wani kuduri a hukumar na kirkirar rumfunan zabe har 30,000."

Ya kuma ce ba wani rufa-rufa a hukumar, kuma idan har za su yi wani abu, dole su fitar da dalilai da bayanai, tare da bin matakai na abin da doka ta aminta da su.

Tuni dai hankulan jama'a a Najeriyar ya fara karkata a kan zaben na 2019.

Baya ga matasa wadanda ke da burin ganin an sa hannu a dokar da za ta rage shekarun tsayawa takara, wasu kuma tsokaci suka fara yi a kan shirye-shiryen gudanar da sahihin zabe.

Bayani kan zaben 2019

  • INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019.
  • Za a fara da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar Tarayya.
  • Daga baya kuma za a yi na gwamnoni da na 'yan majalisun jiha.
  • Hukumar zaben ta yi ikirarin tabbatar da sahihin zabe.