'Masu ikirarin jihadi' sun fille kan mutane a Mozambique

Sojoji na gadi a Mozambique Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An tsaurara matakan tsaro a lardin Cabo Delgado tun da aka fara hare-haren da aka ake ganin masu kaifin kishin Islama ne suka fara kai wa a watan Oktoba.

Hukomomi sun ce wasu da ake zargin masu kaifin kishin Islama ne sun fille kan akalla mutane 10 a arewacin Mozambique.

An rawaito cewa yara na cikin wadanda aka kai wa hari a kauyen Monjane a lardin Cabo Delgado, wata cibiyar binciken albarkatun kasa.

Tun bara ne dai wata kungiyar masu tayar da kayar baya take kai hare-hare a yankin.

An yi imanin cewa kungiyar na samun miliyoyin daloli daga sayar da katako da wasu ma'adinan kasa.

An kafa kungiyar da aka sani da suna al-Shabaab ne a shekarar 2015 a matsayin wata kungiya ta addini, amma kuma ba ta da alaka da kungiyar masu ikirarin jahadi na Somaliya, wadda ke da irin sunanta.

Daya daga cikin wadanda harin karshen makon ya shafa shi ne shugaban kauyen Monjane village, kamar yadda wani mazauna wurin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Ya ce, "Sun yi hakon basaraken ne saboda bayanai da yake bayarwa ga 'yan sanda game da inda al-Shabab ke buya a gandun daji."

Binciken baya-bayan nan ya gano cewa mambobin kungiyar, da wani lokaci ake kira al-Sunna, sun kasance masu bin wani mai wa'azi dan Kenya wanda aka kashe a shekarar 2012.

Mabiyansa sun nufi kudu, suka zauna a Kibiti a kudancin Tanzania, kusa da kan iyakar Mozambique.

'Yan sanda sun kama mutane fiye da 200 dangane da hare-haren masu tayar da kayar bayan da aka fara watan Oktoba.

A makon jiya, hukumomi sun sake bude masallatai shida bayan hare-haren, kuma bayan sun raba gari da kungiyoyin masu dauke da makamai.

Labarai masu alaka