Papua New Guinea 'za ta haramta amfani da Facebook'

Shugaban Facebook Mark Zuckerberg a gaban majalisa a Amurka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Facebook na fuskantar suka kan gazawarsa wajen dakile labaran karya.

Papua New Guinea za ta haramta yin amfani da shafin Facebook har tsawon wata daya domin gano masu shafukan bogi tare da nazarin tasirin shafin intanet a kasar.

Ministan sadarwa Sam Basil ya ce za a gano masu amfani da hotunan batsa da kuma ma su yada labarin karya.

Kuma ya ce kasar na nazarin mallakar nata shafin sada zumunta na kanta a madadin Facebook.

Facebook ya fuskanci bincike bayan bankado badakalar Cambridge Analytica, yayin da kamfanin ke fuskantar suka kan gazawarsa wajen dakile labaran karya.

Ko da yake kimanin kashi 10 ne daga cikin 100 na mutanen Papua New Guinea ke amfani da intanet, amma duk da haka kasar ta zafafa mataka kan ayyukan intanet.

Gwamnati za ta yi amfani da wa'adin wata daya da ta haramta amfani da Facebook domin yin nazarin girman yadda ake amfani da Facebook tare da hukunta wadanda suka saba dokar Intanet da aka kafa a 2016.

Mista Basil ya shaida kafar yada labaran kasar Post-Courier cewa: "Lokacin zai bada izinin tattara bayanai don gano masu amfani da shafukan bogi, da masu saka hotunan batsa, da kuma ma su yada labarai da bayanai na karya."

Samun yawaitar "labaran bogi" ya zama babban kalubale musamman ga kafanonin fasaha a duniya. Suna shan suka kan gazawarsu wajen sanar da mutane game gaskiyar bayanin da aka wallafa.

Ministan ya ce suna diba yiyuwar kirkirar sabon shafin sada zumunta ga al'ummar Papua New Guinea domin amfani da shafuka na gaskiya.

Labarai masu alaka