Kalaman Buhari kan wutar lantarki sun jawo ce-ce-ku-ce

Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Presidency
Image caption A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya cika shekara uku a kan mulki

'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi kan wutar lantarki a jawabinsa na ranar Dimokradiyya.

Shugaban ya ce an samu ci gaba ta fuskar samar da hasken wutar lantarki yayin da yake yi wa 'yan kasar jawabi a ranar Talata, wato ranar da gwamnatinsa ta cika shekara uku a kan mulki.

"'Yan Najeriya suna ba da labarin yadda wutar lantarki ta inganta da kuma yadda suka rage amfani da janareto," in ji shugaban.

Har ila yau ya ce a halin yanzu kasar tana samar da "MegaWatt 7,500"- an samu ci gaba daga MegaWatt 5,222.3 wanda ta samar a watan Disambar 2017.

BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukan sada zumunta bayan mun bukaci sanin ra'ayinsu game da ikirarin shugaban a shafinmu na Facebook.

Yayin da wasu 'yan kasar suka musanta ikirarin shugaban, wasu kuma sun gasgata ikirarin shugaban.

Asy Kano:"Toh ni dai gani a gidana babu wutar lantarki tun safe, har zuwa yanzu tara na dare.. Dama mun Saba sai 12 dare suke kawowa su dauke 3 ko 4 na asubahi. Dole muke neman fetur domin mu tayar da inji saboda azumi ga kuma yara kanana basa iya barci saboda zafi ..mu dai kam bamu ga wata ci gaba ba akan harkar wutar lantarki a Najeriya."

Amma Zubairu Bello gasgata kalaman shugaban ya yi:

"Kwarai kuwa, zancen Shugaba Buhari gaskiya ne. An samu ci gaba a bangaren wutar lantarki. Kuma ina fatan kamfanin wutar lantarki ya koma karkashin ikon gwamnatin tarayya a maimakon 'yan kasuwa."

Godiya Markus kuma cewa ya yi:"A gaskiya mu har yau babu wani canji dangane da wutar lantarki. Mu a Tafawa-Balewa da ke jihar Bauchi mun manta ranar da aka kawo wutar lantarki.Yanzu haka a babban asibitin gwamnati na kwana, amma sai yawan sauro. Kai ko dakin ajiye gawa janareta ake amfani da shi."

Amma Suleiman Issa ya ce a inda yake suna samun wuta:

"Wannan gaskiya ne saboda a nan Lagos a inda nake zama a Opebi a Ikeja. Yau fiye da mako daya a wuni da wuta a dauke wuta sau daya, kafin ka ta da janarato an kawo wutar saboda haka duk wanda ya ce ba'a samu cigaba ba sai dai ko ta wani fannin daban.

Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - kuma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na Facebook:

Labarai masu alaka

Karin bayani