'Ana share ba-haya da hoton shugaban kasar Turkmenistan'

JARIDUN Turkmen Hakkin mallakar hoto Alternativnnyy Novosti Turkmenistana
Image caption Yana da wahala a iya samun jaridar Turkmenistan da babu hoton shugaban kasar Gurbanguly Berdimuhamedov

'Yan sanda a kasar Turkmenistan na gudanar da bincike a wuraren da ake ba-haya domin gano ko ana amfani da jarida da ke dauke da hotun Shugaban kasar Gurbanguly Berdimuhamedov wajen share ba-haya.

Rundunar 'Yan sandan yankin yammacin Balkan ta bukaci jami'anta su shiga wuraren da aka kebe na jama'a domin ba-haya da kuma gidaje masu zaman kansu, domin tabbatar da ko ana share ba-haya da hoton shugaban kasar.

Kafar Fergana.ru ta Rasha da ke watsa labarai a intanet kuma da ke bayar da rahotanni kan lamurran Turkmenistan ta ce an umurci 'yan sanda su tsinto hotunan shugaban a bola da aka share ba-haya da su domin tabbatar da gaskiyar al'amarin.

"Akwai jami'i na musamman da aka ajiye a wuraren zubar da bola don gudanar da bincike, musamman takardar jarida mai dauke da hoton shugaban da aka goge ba-haya da ita, saboda ya sanar da 'yan sanda," in ji jaridar ta Fergana.

Ta kara da cewa, duk wanda aka kama da laifin share ba-haya da hoton shugaban kasar zai fuskanci gargadi mai tsanani.

Sai dai a cewar shafin intanet na Alternativnnyy Novosti Turkmenistana websiteakwai yiyuwar gargadin zai shafi mutane da dama, saboda yadda tabarbarewar tattalin arziki ya sa ba su iya kashe kudi domin sayen tolet fefa, takardar da ake share ba-haya.

"Me zai sa ka saye tolet fefa bayan kana da tarin jaridu a ajiye wadanda ake tilastawa mutanen Turkmenistan su saya," a cewar rahoton jaridar.

Rahoton ya kara da cewa yana da wahala a kaucewa amfani da hoton shugaban kasar saboda yadda hotunansa suka mamaye jaridun kasar.

Wannan na zuwa bayan kame yara da dama kan laifin wasa da hotunan Mista Berdimuhamedov.

Kafar Azatlyk ta rediyo ta ce an kama yaran ne saboda sun tattake hoton Mista Berdimuhamedov a yayin da suke wasa.

Hakkin mallakar hoto Turkmen Government
Image caption Tun 2007 Mista Berdimuhamedov ke mulki a Turkmenistan

Labarai masu alaka