Yadda kwalara ke yaduwa a Arewa maso Gabashin Najeriya

Map din kwalara

Jihohin arewa maso gabashin Najeriya na fama da barkewar annobar cutar amai da gudawa wato kwalara, inda fiye da mutum 1,000 suka kamu, wasu mutanen 31 kuma suka rasa rayukansu tun daga watan Fabrairu.

Jihohin Borno da Yobe da Adamawa dai har yanzu suna fama da annobar, kuma al'amarin na kara muni a baya-bayan nan.

Mutum 482 ne suka kamu da cutar a jihar Adamawa, inda mutum 13 suka mutu.

Annobar cutar ta barke a jihar Yobe ne cikin watan Maris, kuma mutum 404 ne suka kamu yayin da 15 suka mutu ya zuwa ranar 21 ga watan Maris.

A jihar Borno kuwa, annobar ta barke ne a ranar 13 watan Fabrairu, kuma adadin da aka tattara zuwa ranar 20 ga watan Mayu ya nuna cewa mutum 19 ne suka mutu, dukkansu kuma daga yankin Kukawa.

Shugaban Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu, a wata sanarwa da ya fitar ya ce, ruwan saman da ya fara sauka ne ya sa aka samu karuwar masu fama da cutar.

A farkon watan Mayu ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da dala miliyan biyu ta hannun Asusun Agaji na Najeriya, domin shawo kan cutar kwalarar da ta barke a arewa maso gabashin kasar, wadda ake tsoron idan ba a magance ta ba za ta iya shafar dubban mutane.