Fasto ya nemi mabiyansa su saya masa jirgin sama na $54m

Dassault Falcon 7X on approach to the runway of Le Bourget airport during the Paris Air Show, 2011

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jesse Duplantis ya ce jirgin zai kasance na amfanisa ba, amma maimakon haka "zai kasance na ikilisiyar ne"

Wani fasto mai wa'azi a talabijin a Amurka ya nemi mabiyansa domin sayen jirgin samansa na hudu- domin Yesu "ba zai hau jaki ba".

Jesse Duplantis ya ce Allah Ya sanar da shi ya sayi jirgi samfurin Falcoln 7X kan kudi dala miliyan 54.

Ya kara da cewa shi bai so sayen jirgin ba daga farko, amma ya ce Ubangiji ya gaya masa cewa: "Ban sa ka ka saya da kudinka ba. So nake kawai ka yi imanin cewa za ka samu ."

Duk da cewa ba wani abun a zo a gani ne ace masu wa'azin Kirista suna da jirage na kansu ba, wannan kiran ya janyo ce-ce-ku-ce.

Masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter sun nuna rashin yarda game da kiran, inda da yawa daga cikinsu suka yi ta kawo ayoyin baibul da ke gargadi kan hadama da "manzannin karya", ko kuma suna nuna cewa kudin zai fi amfani wajen taimaka wa talakawa.

A wani jawabi na bidiyo da aka wallafa a shafinsa na intanet, - Mista Duplantis mai shekara 68 ya bayyana cewa : "Kun sani, ina da jiragen sama uku na kaina, na yi amfani da su kuma ina kona su ne kawai saboda Yesu Almasihu.

"A yanzu, wasu mutane suna da imanin cewa ka da masu wa'azi su sayi jirage. Na yi imanin cewar dole masu wa'azi su yi amfani da ko wacce murya, ta ko wacce hanya domin yada bisharar nan ga duniya."

Yayin da yake tsaye a gefen hotunan jiragensa na yanzu, ya ce jirgin da ya saya shekara 12 da suka wuce ba zai ishe shi aikin ikilisiyarsa ba."

Wani hoto da aka nuna a cikin bidiyon kuma ya nuna mai wa'azin yana tsaye da jirage ukun a saman wani rubutu mai cewa "Ba batun abun da aka mallaka ba ne, batu ne na abubuwan da aka bai wa fifiko."

Mista Duplantis ya kafa hujjar cewa Yesu ya ce wa mutane su "shiga cikin duniya domin yada bushara ga ko wacce halitta, a yanzu ta yaya za ka yi wannan? Ba zan iya irin dadewar da zan iya tafiya ta mota ko jirgin ruwa ko jirgin kasa ba, amma zan iya tafiya ta jirgin sama".

A shekarar 2015, Mista Duplantis ya fito a wani bidiyo tare da wani mai wa'azi, Kenneth Copeland, inda mista Copeland ya bayyana tafiye-tafiye a cikin jiragen fasinja a matsayin kasancewa "cikin wani dogon bututu tare da wasu aljanu".