Kotu ta tura tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, gidan yari

Ramalan Yero

Asalin hoton, Facebook/AbdurRahman Abubakar

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan jihar Alhaji Muktar Ramalan Yero a gidan yari.

Mai magana da yawun hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC, Wilson Uwajeren ya tabbatar wa da BBC batun.

A ranar Alhamis ne kotun ta bayar da wannan umarni bayan da EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun.

Ana tuhumar tsohon gwamnan ne da laifuka hudu da suka hada da halatta kudin haram da hada baki wajen aikata babban laifi da karkatar da dukiyar al'umma da kuma cin amana.

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen da aka yi masa.

An yi ta yada hoton tsohon gwamnan dauke da allon da aka rubuta sunansa da tuhume-tuhumen da ake masa a kafafen sada zumunta.

Asalin hoton, Facebook/EFCC

Hakazalika kotun ta bayar da umarnin tsare wasu mutum ukun da ake tuhumarsu tare da tsohon gwamnan da suka hada da tsohon Ministan Makamashi Nuhu Wya da tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kaduna Hamza Ishaq da kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Haruna Gaya.

Sai dai su ma duk sun musanta tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Bayan alkalin kotun Mai Shari'a Mohammed Shuaibu ya yanke wannan hukuncin, lauyan Ramalan Yero ya nemi da a ba da belin wanda yake karewar, amma bukatar tasa ba ta samu shiga ba.

Alkalin kotun ya dage zaman sauraron shari'ar har zuwa ranar 6 ga watan Yuni don yanke hukunci kan bukatar neman belin.

Mista Uwajeren ya ce a ranar Juma'ar da ta gabata ne EFCC ta gayyaci Ramalan Yero da sauran mutanen don su yi bayani kan zargin karkatar da kimanin naira miliyan 750 wajen yakin neman zabe.