Buhari ya sa hannu kan dokar bai wa matasa damar tsayawa takara

Bayanan bidiyo,

Shugaba Buhari lokacin da yake sanya hannu kan sabuwar dokar ranar Alhamis

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar nan ta bai wa matasa damar tsayawa takara.

Kudirin ya ba matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar.

Haka zalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar Tarayya.

Sai dai babu sauyi a shekarun wadanda ke neman kujerar gwamna ko kuma sanata - wato za su fara ne daga shekara 30.

A watan Yulin 2017 ne Majalisar dattawan kasar ta amince da kudirin da zai bai wa matasa damar tsayawa takara a mukaman shugaban kasa da gwamna da majalisun dattawa da na wakilai.

Ana ganin matakin na shugaban kasa, wani gagarumin ci-gaba ne, kuma wasu matasan kasar sun nuna farin cikinsu kan sauyin da aka samu.

A baya dai mutane da dama sun nuna shakku kan ko shugaban zai amince ya sa hannu kan dokar.