Denmark ta haramta wa mata saka nikabi a bainar jama'a

Denmark

Asalin hoton, Getty Images

Kasar Denmark ta amince da dokar haramtawa mata saka nikabi a cikin bainar jama'a.

'Yan majalisar dokoki ne suka amince da kudurin haramcin, da za a fara amfani da shi a watan Agusta mai zuwa.

Kasashen Turai da dama ne suka kafa dokar haramta wa mata saka nikabin.

Duk matar da aka samu ta lullube fuska da sunan nikabi za a ci ta tarar dala 160 a Denmark.

Kudin tarar kan iya rubanya idan aka sake samun mace da sake aikata laifin.

Wannan matakin na Denmark dai ya shafi matan musulmai ne kai-tsaye wadanda ke rufe fuska da nikabi ko burka.

Ko da yake, dokar ba ta ambaci matan musulmi ba, amma ta ce, "duk wanda aka kama ya yi amfani da wani mayafi da ya rufe fuska a bainar jama'a za a ci tarar shi.

Bayan amincewa da dokar, Ministan Shari'ar Denmark Søren Pape Poulsen ya ce "Babu dalilin da zai sa wasu su rufe fuskarsu, dole ne mu iya ganin fuskar juna, domin shi ne al'adar kasar Denmark."

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bayyana dokar a matayin wadda ta sabawa 'yancin mata.

A shekarar da ta gabata wata kotun kare hakkin dan adam a Tarayyar Turai ta zartar da hukunci irin wannan a Belgium, tare da cewa haramcin bai sabawa dokokin kungiyar ba kan hakkin dan adam.

Kasar Faransa ita ce kasa ta farko da ta fara haramtawa mata sanya nikabi a shekarar 2011.