Zakuna biyu da damusa uku sun tsere daga Gidan Zoo a Jamus

The lions Malor and Lira (front) in Eifel zoo in 2016 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zakunan wadanda ake kira Malor da Lira a Gidan Zoo na Eifel zoo a shekarar 2016. Babu tabbas ko suna cikin wadanda suka tsere din

Hukumomi a Jamus sun ce an samu nasarar kamo zakuna biyu da damusa ukun da suka tsere daga gidan ajiye namun daji a wani yanki da ke yammacin kasar. T

An gano dabbobin ne a harabar Gidan Zoo din da ke Lünebach bayan da aka yi amfani da jirgi maras matuki wajen neman su.

A ranar Juma'a da safe ne 'yan sandan kasar suka bayar da sanarwar tsarewar dabbobin tare da shawartar mutane su kasance a gidajensu, su kuma kira 'yan sanda idan sun ga wani abu.

Wani jami'i da ke yankin ya kuma shaida wa kamfganin dillancin labarai na AFP cewa wata muguwar dabba da ake kira bear ma ta tsere daga gidan namun daji na Eifel, amma an harbe ta.

Kafofin yada labaran Jamus sun ce dabbobin sun balle ne bayan da aka sheka ruwa kamar da bakin kwarya cikin dare, wanda ya jawo ambaliyar da ta lalata keji da suke ciki.

Tawagar 'yan sanda da jami'an kashe gobara da likitocin dabbobi ne suka yi ta aikin neman dabbobin.

Gidan Zoo din mai girman eka 30, wanda mallakin iyalan Wallpott ne, yana dauke da kusan dabbobi 400 daban-daban, da suka hada da zakuna da damusa.

A cewar shafin intanet na Gidan Zoo din an fara bude shi ne a shekarar 1965 da karnuka da jakuna kawai, kuma mutum 70,000 ke ziyartarsa duk shekara.

Tserewar dabbobin ta baya-bayan nan dai ta zo ne shekara biyu bayan da wasu zakuna biyu suka tsere daga Gidan Zoo na Leipzig da ke gabashin Jamus.

Labarai masu alaka