‘Yan biyun da ke rayuwa a hade sun mutu

'Yan biyun da suke rayuwa a hade

Kasar Tanzania na cikin alhinin rasuwar tagwayen nan da suke rayuwa a hade da suka shiga zukatan al'ummar kasar wato Maria da Consolata Mwakikuti.

Tagwayen sun mutu ne suna da shekara 22 da haihuwa sakamakon matsalar numfashi da suka samu.

Matasan tagwayen na amfani da wasu sassan jikinsu tare kamar hanta da huhu, amma kuma suna da zuciya biyu, kuma daga kansu zuwa kafadarsu ma a rabe ya ke.

Sun fara rashin lafiya ne tun a karshen shekarar bara inda suka samu matsalar da ta shafi numfashi, sai aka kwantar da su a asibiti, sun kuma mutu a ranar Asabar din data gabata.

Labarin mutuwarsu ya girgiza al'ummar kasar ta Tanzania kwarai da gaske, saboda yadda ake kaunarsu.

Mutane da dama a kasar sun aika da sakon ta'aziyyarsu ga iyalai da 'yan uwan mamatan da kafafan sada zumunta.

Shima shugaban kasar, John Magufuli , ya wallafa sakon ta'aziyyarsa ta shafinsa na twitter yana mai cewa, ' Ina mai matukar alhinin rasuwar Maria da Consolata, saboda suna da burin taimakawa kasa'.

A cikin wata hira da suka yi da BBC a bara, tagwayen sun ce idan suka kammala karatun jami'arsu, suna son zama malaman makaranta.

Tagwayen suka ce ' Zamu rinka amfani da komputa wajen koyarwa'.

Image caption Tagwayen sun ce suna fatan wata rana su yi aure

Al'ummar kasar sun ce za su ci gaba da tunawa da tagwayen saboda irin jajircewarsu wajen neman ilimi duk da kalubalen da suka fuskanta.

Tagwayen sun samu tallafin karatunsu daga karamar hukumarsu da kuma mutane da dama gami da kungiyoyi masu zaman kansu.

Maria da Consolata, ba su amince ayi musu aiki a raba su ba, sun taba shaidawa BBC cewa, suna fatan su auri miji daya wata rana.

Tagwayen sun girma ne a wajen mabiya darikar Katolika, wadan suka dauke su tun suna jarirai bayan iyayensu sun mutu.

Labarai masu alaka

Karin bayani