Fursunoni 180 sun tsere daga gidan yari a Najeriya

gidan yari

Asalin hoton, Getty Images

Wasu fursunoni da dama sun tsere daga gidan yari a Minna baban birnin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Hukumar gidan yarin jihar ta ce al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe takwas na dare, a gidan yarin mai matsakaicin tsaro da ke yankin Tunga.

Sanarwar da hukumar ta aike wa manema labarai ta ce wasu 'yan bindiga dadi ne suka kai hari gidan yarin inda suka yi ta musayar wuta da masu gadin wajen, har suka samu damar shiga.

Kawo yanzu an sake kama 30 daga cikinsu, yayin da ake ci gaba da neman 180.

Al'amarin ya jawo mutuwar wani ma'aikacin gidan yarin daya da kuma dan acabar da ya dauko shi, a yayin da suke daf da shiga gidan yarin, inda ma'aikacin zai shiga aikin dare.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Abdulrahman Bello Dambazau ya isa garin na Minna don ganin irin barnar da lamarin ya jawo.

Sanarwar ta ce a yanzu hankula sun kwanta kuma hukumomin tsaro na ci gaba da "aiki ka'in da na'in don tabbatar da cewa an kamo dukkan wadanda suka tsere."

Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito Minista Dambazau yana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya na gina gidan yari mai daukar mutum 3000 a ko wacce shiyya ta kasar, za kuma a dauki ma'aikata 6000, amma ya tabbatar da cewa akwai karancin tsaro a gidan yarin na Minna.

"Akwai matsalar rashin tsaro da ya kamata a shawo kanta a gidajen yari kamar rashin isassun ma'aikata da kuma cunkoso," in ji minsitan a cewar PR Nigeria.