Shin wa ya fi kima tsakanin Saniya da Mace a Indiya?

Shin wa ya fi kima tsakanin Saniya da Mace a Indiya?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mata a Indiya na sanya fuskar shanu ta roba suna kuma tambayar mutane bayani kan cin zarafin da mata ke fuskanta.

Hakan yana cikin wani aiki na nunin hotuna da wani mai daukar hoto Sujatro Ghosh ya kirkiro, wanda ke cewa “ana fi bi wa saniya hakkinta a kan lokaci fiye da macen da aka yi wa fyade, saboda mabiya addinin Hindu sun dauki saniya da daraja kuma abar tsarkakewa.”

Ana samun karuwar kungiyoyin kato da gora masu kare shanu tun bayan da jam’iyya mai mulki ta mabiya addinin Hindu BJP ta karbi mulkin kasar a 2014.

Ana yawan samun labaran cin zarafin mata a Indiya, kuma wata kididdigar gwamnatin kasar ta nuna cewa ana yi wa mace fyade cikin duk minti 15.