Kada ya cinye wani fasto yana wankan tsarki a kogi

A close up photo of a crocodile's head Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kadodi na yin rayuwa ne a cikin tafkuna da koguna

Wani kada ya kashe wani fasto a yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarkin addinin kirista a wani kogi a kudancin Habasha.

Fasto Docho Eshete yana yi wa wasu mutane 80 ne wankan tsarkin na shiga addinin kirista a ranar Lahadi da safe a Tafkin Abaya da ke garin Araba Minch a gundumar Merkeb Tabya.

Mazauna garin da 'yan sanda sun shaida wa BBC Amharic cewa ana cikin wankan sai kawai wani kada ne ya sudado ya cafki faston.

Pastor Docho ya mutu sakamakin cizon da kadan ya yi masa a kafafu da baya da hannayensa.

"Ya kammala wa mutum na farko wankan, ya zo kan na biyu. Kwatsam, sai wuf wani kada ya fito ya cafko faston nan," a cewar wani mazaunin Ketema Kairo.

Wani dan sanda Eiwnetu Kanko yace, duk da irin kokarin da masunta da mazauna yankin suka yi don cetonsa, ba a samu an ceto faston ba.

Sun yi amfani da komar kamun kifi don hana kadan dauke gawar faston zuwa karkashin kogin.

Amma kadan ya tsira ba tare sun samu damar kashe shi ba.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka