An jinjinawa 'yar sanda saboda shayar da jaririn da aka yasar

'Yar sanda mace rike da jaririn da aka yasar bayan ta shayar dashi

An jinjinawa wata jami'ar 'yan sanda saboda shayar da wani jariri da aka yasar a jihar Karnataka da ke kudancin kasar India.

'Yar sandar ta ce ' Ba zan iya jurewa na bar jaririn a halin da aka tsince shi ba, da naji kukansa sai naji kamar da na ne ya ke kuka, don haka dole na bashi nono ya sha'.

Mahukunta a jihar sun ce, wani mai shago ne ya kira su a waya ya sanar da su cewa ga wani jariri fa an yasar yana kuma ta kuka a kusa da wani waje da ake gini a babban birnin jihar Bangalore.

Mazauna garin sun yi wa jaririn lakabi da 'dan gwamnati'.

Jami'ar 'yar sandar da ta shayar da jaririn mai suna Archana, ta shaida wa BBC cewa, ba ta jima da haihuwa ba, shi ya sa ta ji zafin yadda aka yasar da jaririn.

Abokanan aikinta sun jinjina mata kwarai da gaske saboda namjin kokarin da ta yi na hanzarta shayar da jaririn ta na ganinsa, inda suka ce hakan ya taimaka wajen ceto rayuwarsa.

Tuni dai aka kai jaririn asibitin domin duba lafiyarsa saboda yanayin da aka tsince shi a wata bola d ake wajen garin domin lafiyarsa.

Bayan kammala bincikar lafiyarsa, an kai shi gidan kula da marayu domin a ci gaba da kula dashi yadda yakamata.

Labarai masu alaka