Bama-bamai sun ruguza wani masallacin 'yan Shi'a

Iraqis inspect the aftermath of explosions that destroyed a mosque in Baghdad's Sadr City district (7 June 2018) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masallacin da abubuwan fashewa suka lalata wuri ne da magoya bayan malamin Shi'ar nan Moqtada Sadr ke sallah

Abubuwan fashewa sun kashe a kalla mutum 17 tare da jikkata wasu mutanen 80, tare da lalata wani masallaci a babban birnin kasar Iraki, in ji majiyoyin lafiya.

Gwamnatin kasar ta ce fashe-fashen na daren Laraba sun faru ne sanadiyyar fashewar ma'ajiyar makamai a unguwar 'yan Shia da ke birnin Sadr.

Sai dai ta bayar da bayanin ainihin inda ma'ajiyar makaman take ba, amma wasu jami'an tsaro sun ce a cikin masallacin ne.

Magoyan bayan malamin Shi'ia Moqtada Sadr su ne suke amfani da masallacin.

Mista Sadr ya jagoranci wani kawance na kishin kasa wanda ya hada da wasu kungiyoyin da ba na addini ba a zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi a watan jiya, inda ya ci 54 daga cikin kujeru 328.

Ya kuma jagoranci mayakan da suka yaki dakarun Amurka bayan sun far wa Iraki a shekarar 2003, amma a shekarun baya-bayan nan yana taimaka wa sojojin Irakin da Amurka ke mara wa baya a yakin da suke yi da 'yan IS masu ikirarin jihadi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin ta ce tana bincikar musabbabin fashewar
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kananan yara da mata na cikin wadanda lamarin ya shafa

Wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewar tarin makaman na wata kungiyar 'yan bindiga ce, kuma makaman sun hada da gurneti da rokoki.

Gwamnatin ta ce ana kan bincike domin gano abin da ya sa ma'ajiyar makaman ya fashe, amma wani rahoto ya ce an yi imanin cewar ya faru ne a lokacin da ake son a kai makamai wata motar da aka ajiye kusa da wurin.

Hotunan da aka dauka bayan fashe-fashen sun nuna cewa fashewar makaman ta daidaita masallacin tare da lalata gidajen da suke kusa da kuma wasu gine-ginen.

Labarai masu alaka

Karin bayani