Najeriya ta cika wa Bonfrefe Jo alkawari bayan shekara 22

Bonferere Jo Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Najeriya ta cika wa tsohon kocin kwallon kafar kasar Bonfrere Jo, alkawarin gida bayan shekara 22.

Kocin dan kasar Holland, wanda ya jagoranci tawagar 'yan kwallon Najeriya 'yan kasa da shekarar 23 ga nasarar lashe zinari a wasannin Olympics a Atlanta a 1996, ya karbi kyautar da gwamnati ta yi masa alkwari shekara 22.

Jo Bonfrere ya karbi makullin wani gida mai daki uku a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, daga ministan makamashi da ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola.

Wannan matakin ya cika alkawarin da gwamnatin marigayi Sani Abacha ta yi.

Abacha ne yake kan karagar mulki a lokacin da Najeriya ta lashe zinari a fagen kwallon kafa a wasannin Olympics bayan ta doke Argentina da ci 3-2 a Atlanta 1996.

Labarai masu alaka