'Ya kamata a daina sa wa mata ido idan ba sa azumi'

mata

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabata ne mata Musulmai a wasu sassan duniya musamman Turai da Gabas Ta Tsakiya, su ka yi ta bayyana yadda suke fuskantar matsin lamba daga wajen mutane a lokacin da ba sa azumi saboda zuwan jinin al'ada.

Matan dai sun yi ta wallafa hakan ne a shafukan sada zumunta da muhawara wasu kuma sun shaida wa BBC News yadda suke fuskantar kalubale yayin da suke al'ada da Ramadan.

Wasu sun ce su kan buya daga idon 'yan uwansu maza domin ka da a gansu ko kuma su yi karya saboda suna jinin al'ada.

BBC Hausa ta ji ta bakin wasu mata a Najeriya ta manhajar Whatsapp, kan irin dabarun da suke yi don cin abinci ba tare da an gansu ba a yayin da suke al'ada da azumi.

Ga dai irin amsoshin da suka bayar, amma sun bukaci mu boye sunayensu.

"Ni dai a wajena ba na jin wata kunya ko wani dar-dar idan zan ci abinci lokacin azumi yayin da nake al'ada, saboda jinin haila ai abu ne da kowa ya san ana yi. Kawai dai ba zan fito kan titi in ci abinci ba ne, amma yadda na saba cin abincina kafin azumi to haka nake yi yayin da nake hutun sallah da azumin.

Ko a gaban 'yan gidanmu maza ne ba ruwana. Wani sa'in kamar da gangan ake tambaya ma me ya sa ba kya azumi? Sai kawai na ce, ba na sallah ne," a cewar mace ta farko kenan.

Mace ta biyu ta ce: "Ni dai ba na jin wata kunya don na ci abinci a gaban 'yan gidanmu, tun da na san yadda Allah ya yi ni mace Ya fi ni sanin wannan abu da ya dora min, kawai dai ba zan fita kwararo na ci abinci ba ne."

Mace ta uku: "Ni ba na jin komai don an ganni ina cin abinci da azumi, matsalata daya ita ce, 'yan sa ido masu yawan tambayar me ya sa ba kya azumi, bayan kuma sun san dalili sarai. Sai kawai na ce musu ban jin dadi ko kuma ina al'ada."

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mace ta hudu ta ce: "Gaskiya abun ba sauki, amma bai kamata mutane su sa mata su dinga jin kamar sun yi wani laifi ba don an gansu su na cin abinci da azumi, hakan bai kamata ba."

Mace ta biyar kuwa cewa ta yi: "Ni kam ba ni da wata damuwa wajen cin abinci da azumi in dai har in dai dama na saba cin abincin gaban wadanda zan ci ko ba azumi ba. Matsalata daya, da zarar na fita daga gida na samu kaina gaban wadanda ban sani ba, to fa sai dai na yi azumin dole na ki cin abinci, don na tsani a yi ta tambaya ta, 'Me ya sa ba kya azumi'?

Babban abun takaicin shi ne sun fa san dalilin sarai amma ba za su fasa tambaya ba. Ni ba wai kunyar ina al'ada nake ji ba, kawai ba na so mutane su fara tunano yadda lamarin yake ne."

Mace ta shida ma ga nata bayanin: "Ni ba wai cin abinci a gaban mutane ne babbar damuwar ba. Ko da za ki buya a wani waje, da zarar an kama ki sai an maki wannan banzar tambayar, 'Me ya sa ba kya azumi?' Bayan zun san amsar. To dole ne sai na yi bayani dalla-dalla?

A gidanmu dai na fi sakewa na ci abincina. Amma gaskiya ya kamata a daina nuna wa mata kyara don an ga suna cin abinci lokacin Ramadan. Tun da dai al'adar nan an halicci yanayin jikinsu da ita ne".

Asalin hoton, Getty Images

Wata kuwa ita a nata ra'ayin cewa ta yi: "Gaskiya ni dai ba na taba iya sakewa na ci abinci ko a gida ko a abakon waje idan ina al'ada lokacin Ramadan. Saboda haka hakuri kaai nake yi na kame bakina kamar kowa."

Yayin da wata Injiniya kuwa ta shaida mana cewa: "Ni kam ba na kunyar cin abinci a gaban ko waye idan ba na azumi.

"Kuma duk wanda ya kalli idona ya tambaye ni dalili zan gaya masa cewa ina al'ada ne ba wani kame-kame. Kuma ko a wajen aiki idan na ji yunwa fuska nake yi kawai na ci abincina. Ai duk baligi ya san dalili."

Me addini ya ce kan hakan?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Malamai sun ce bai kamata macen da ba ta azumi ta ci abinci a gaban yara ba

Wannan muhawara da matan suka yi ta tafkawa ta sa muka tuntubi wasu malaman addini a Najeriya, don jin me Musulunci ya ce kan cin abincin mata yayin da suke al'ada da azumi.

Dokta Zahra'u Umar ita ce Mataimakiyar Kwamada Janar na hukumar Hisbah da ke Kano ta kuma ce komai na rayuwa ya kamata a yi shi bisa tarbiyya ce ta addini ko ta al'ada mai kyau.

"Ai dama a tarbiyyar Musulunci ba a san mace da cin abinci hayam-hayam a kan titi ba. Don haka in dai za ta ci abinci yayin Ramadan saboda halin haila kamar yadda take cin abinci a bayan Ramadan babu laifi.

"Ko da tana ci ne wani ya ganta, ai shi ya kawo kansa wajen ba wai ita ta fita ta tallata kanta ba. Don haka al'ada ce kawai ta Bahaushe ke sa wa a dinga kyarar mata don an ga suna cin abinci da azumi, in ji Dakta Zahra'u.

Ta kara da cewa: "Abun da ba a so shi ne mace ta ci abinci a gaban yara kanana da ba su san mene ne al'ada ba, saboda hakan zai iya rusa sha'awarsu ta yin azumin."

Shi ma wani fitaccen malamin addini a Kanon Sheikh Ibrahim Khalil ya tofa tasa kan wannan batu, kuma yana ganin ma mace na da zabi biyu a lokacin Ramadan.

"Ko dai ta sha magani tun farkon azumin ta yadda ba za ta yi al'ada ba har a gama, ballantana ta fuskanci kalubale wajen cin abinci, ko kuma ta yi azuminta.

"Musulunci bai hana mace mai haila kin cin abinci ba saboda gudun ka da mutane su gani. Ai dama kamata ya yi ko ba lokacin azumi ba mace ka da ta ci abinci a kwararo, amma fa don tana zaune waje daya tana cin abinci wani ya ganta, ai ba ta da laifi.

"To laifin me za ta yi ma bayan Allah ne da Kansa ya dauke mata yin azumin kuma shi ya halicce ta da yanayi na yin haila?," in ji Sheikh Khalil.

Karin labaran da za ku so ku karanta: